Mujallar Wasanni
this is sports page to bring the sports news
26/11/2021
Ralf Rangnick: Manchester United za ta nada dan kasar Jamus rikon kwarya na wata shida.
Rangnick ya kai Schalke karawar daf da karshe a Champions League
Manchester United ta kusan nada Ralf Rangnick a matakin kocin rikon kwarya da zai ja ragamar kungiyar wata shida.
Mai shekara 63 dan kasar Jamus na daf da zama mai horar da kungiyar Old Trafford, sai dai ba zai ja ragamar United wasan da za ta ziyarci Chelsea a gasar Premier League ba ranar Lahadi, sai ya samu takardun izinin aiki a Birtaniya.
United ta cimma yarjejeniya da Rangnick, amma ba ta cimma matsaya da Locomotiv Moscow ba, inda yake aikin jami'in bunkasa wasannin kungiyar.
Hakan ya biyo bayan da United ke neman wanda zai maye gurbin Ole Gunnar Solskjaer wanda ta kora ranar Lahadi, wanda ya yi kaka uku ba tare da lashe kofi ba.
Rangnick ya ci German Cup tare da Schalke a 2011 da kai RB Leipzig karawar karshe a 2019 a dai kofin.
A kakar 2010 ya kai Schalke matakin daf da karshe Champions Legue, wanda ya sha kashi a hannun United, ita kuma kungiyar Ingila ta yi rashin nasara a karawar karshe da Barcelona ta lashe kofin.
United tana ta takwas a kan teburin gasar Premier League, wadda ta sallami Solskjaer, bayan da United ta yi rashin nasara a gidan Watfortd da ci 4-1 ranar Asabar.
Tuni United ta bai wa Michael Carrick aikin rikon kwarya, wanda ya je ya doke Villareal 2-0 a gasar Champions Legue a Sifaniya ranar Talata da hakan ya kai kungiyar Old Trafford zagaye na biyu a gasar Zakarun Turai.
Aley Abs
25/11/2021
Carrick zai fuskanci kalubale a Stamford Bridge ranar Lahadi.
Michael Carrick ya ja ragamar Manchester United ta doke Villareal da ci 2-0 a Champions League a matakin kocin rikon kwarya ranar Talata.
Tsohon dan kwallon United ya karbi aikin jan ragamar kungiyar Old Trafford, bayan da aka kori Ole Gunners ranar Lahadi, sak**akon da Watford ta doke ta da ci 4-1 a gasar Premier League ranar Asabar.
Kungiyar ta ce ta nada Carrick a matakin rikon kwarya na da wani lokaci ko zuwa karshen kakar bana, daga nan ta dauki sabon kocin da za ta bai wa wuka da nama.
Carrick ya kai United zagaye na biyu a Champions League, bayan da s**a yi nasara a kan Villareal ranar Talata a Sifaniya a Champions League.
To sai dai kuma United za ta fuskanci wani kalubale mai zafi a gasar Premier League da za ta ziyarci Chelsea ranar Lahadi.
Ita kuwa Chelsea ta casa Juventus 4-0 ta dare mataki na daya a kan teburin rukuni na takwas karkashin Thomas Tuchel, kuma tana ta daya a kan teburin Premier League.
Manchester United kuwa tana ta takwas a kan teburin babbar gasar Ingila, wadda ta sha kashi a wasa hudu daga biyar baya da ta fafata.
Sai dai Chelsea ta kwan da sanin cewar ta kasa samun nasara a kan United a wasa bakwai a Premier League da kasa cin kwallo a fafatawa hudu daga ciki.
Carrick zai je Stamford Bridge ba tare da kyaftin Harry Maguire ba, wanda aka bai wa jan kati a wasan Watford da kuma Raphael Varane wanda ke jinya - an ci United kwallo 15 a karawa biyar a Premier League abinda Carrick keson mayar da hankali kenan.
Watakila Victor Lindelof, wanda ya taka rawar gani a fafatawa da Villarreal a Sifaniya da Eric Bailly su yi tsaron bayan United, haka kuma watakila mai tsaron baya, Donny van de Beek ya fara taka leda karkashin Carrick.
Aley Abs
25/11/2021
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Mbappe da Bale da Werner da Lacazette da Lingard, Traore da Ziyech.
Dan wasan gaba na Paris St-Germain da Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22, zai iya barin ƙungiyar idan kwantirginsa ya kare a lokacin bazara, inda Newcastle United ta shiga jerin masu sha'awarsa. (Express).
Dan wasan gaba na gefe na Chelsea Hakim Ziyech, dan Moroko mai shekara 28, da kuma dan gaban Jamus Timo Werner, mai shekara 25, sun kasance wadanda Barcelona za ta nema a madadin Raheem Sterling, na Manchester City, idan kungiyar ba ta samu nasarar janye dan Ingilar mai shekara 26 ba a watan Janairu. (ESPN).
Paris St-Germain ta yi watsi da bukatar farko da Manchester United ta gabatar kan kociyanta Mauricio Pochettino
(Manchester Evening News).
Tsohon kociyan Tottenham, Pochettino, mai shekara 49, sai ya jira akalla wata shida kafin ya k**a aiki da United. (Star).
Manchester United din ta tattauna da tsohon kociyan Borussia Dortmund Lucien Favre da tsohon mai horas da Lyon Rudi Garcia kan aikin wucin-gadi. (Telegraph).
Wadanda kungiyar ta Old Trafford take zawarci da aikin na rikon kwarya har da tsohon kociyan RB Leipzig Ralf Rangnick da tsohon kociyan Roma Paulo Fonseca. (Mail).
A cire wani zane na hoton kociyan United da aka kora Ole Gunnar Solskjaer daga Old Trafford. (Sun).
Liverpool da Barcelona na sha'awar dan gaban Chelsea Christian Pulisic, mai shekara 23, amma kuma Blues ba za ta sayar da shi ga wata kungiya abokiyar hamayyarta ba a Premier, kuma ita Barcelona ba ta da yuro miliyan 50 da za ta sayi dan wasan gaban na gefe dan Amurka. (El Nacional).
Chelsea ta tattauna da dan bayan Fenerbahce da Hungary Attila Szalai, mai shekara 23. (Football Insider).
Wolves za ta saurari masu bukatar sayen dan gabanta na gefe dan Sifaniya Adama Traore, mai shekara 25, a watan Janairu. (Football Insider).
Aley Abs
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Kwanar Dala Road
Kano