HeartTalk

HeartTalk

Share

Daily relationship truths, advice & real-life stories.

18/06/2026

Kalaman soyayya 🥰

18/06/2026

*🌾DAGA RUGA NAKE🌾*

*NA*
*A'ISHAT SALISU UMAR NA DANGO*
*(Mrs Awwal)*

*HABIBTYN JAJIRTATTU CE* 🥰🥰

020

Sai da ta ƙurɓi lemun exotic ka min cikin dakewa, don kaɗan ya rage ta sa ki dariya ganin yadda ya wani zaro ido waje. '' Ya Ashrap wani laifi na yi ne? Ko dai na ɓata ma rai ne ban sani ba? Dan Allah ka yi haƙuri ka san ɗanAdam ajizi ne.'' Ta furta cikin marairai ce murya tamkar ba ita ba.

'' Amm.. Uhmm.'' Sai kuma ya yi shiru gudun kada ya yi wata magana kuma, ta za mo laifi a gurin aljanunta.

Ajiye Flash ɗin ta yi, ta miƙe wurinsa ta nufa baya-baya ya farayi don a tsorace yake da ita, tana ƙarasawa ta durƙusa ƙasa ledojin da ke zube a ƙasa ta shiga kwashewa. '' Ya Ashrap me kuma muka samu yau? Kuma ba ka amsan maganata ba ko dai baka son na je sai na hakura ka ga sai na je gidan Maamah.''

Maamah da jin zancen Dagori ya sa ta kware da abincin bakinta tana zaro ido ta buÉ—e baki da niyyar magana sai ta ji Innaya na faÉ—in.

'' Ke! Mai suna wai ke! Har sai yaushe za ki yi hankali ne? Ta ya za ki wani tsare su da dole sai sun amince kin je gidansu ai duk saurin unguwar zoma ta jirayi naguÉ—a ai, to ni na ce; babu idan za ki tun da ke sam ba hankali jikinki na lura tun da kika lura Ashrap da Maamah suna tsoronki ki ke yi wa mutane iskanci, to daga yau sai yau kai! Ashrap ban yarda ka sake siya ma ta komai ba muddin ba ka siyo ba ne tare da 'yan uwanta, aljanu hauka ne da duk za ka wani bi ka susuce akan su ko ba ka san sun fi raina wanda s**a lura ya fi tsoron su ba sun fi yi ma sa iskanci ai.''

Kuka mai sauti Dagori ta saki wanda ba wai na shagwaɓa ba ne daga zuciyarta yake fotowa don ƙiri-ƙiri za ta ga samu ta ga rashi. ''Ta ya na fara sabawa da kayan daɗin da yake siyo min shi ne wannan, tsohuwar za ta zo da wani na ta iya yin don kawai tsabar baƙin ciki wato duniyar nan, ba abun yarda ba ce ace kakarka wanda ta haifi mahaifinka tana yi ma hassada wato ta fison su Ya Ashrap akanta, to ba bama dole ta fi so su ba tun da mahaifinsu ya fi nata kuɗi da komai amma ni ma fa da na wa laifin da lokacin da ake kawo min kayan daɗin nan, ko na ɗan tsakura na ba ta ai da na kashe bakin tsanya, amma sai dai na k**a na cinye kai ka ce tsohuwar mayya na tabbatar yanzu hatta Salame sai ta yi murna yoo ko ita ba sam ma ta nake ba dalle kuma su Inty.''

Ta yi maganar a zuciyarta, ta sake fashewa da kuka mai tsuma zuciya tamkar wanda aka yi wa duka.

" Haba Innaya kin sanfa ba'a ɓawa mai wannan matsalar rai yanzu sai ki tsokanosu.'' Mami ta furta don sam ba ta ƙaunar abun da zai sake sa aljanun Dagori su tashi, don ranar ita kawai ta san halin da ta shiga silar hakan.

'' Asiya bari wannan zancen yau duk s**a tashi ubansu za su ci ai dan hayaƙi zan yi ma su wanda ko ba suwa Allah sai sun fita.''

Dagori da jin zancen Mami ya sa da za ta zuɓe ƙasa sai kuma, ta ji zancan hayaƙi wanda Nene ta taɓa yi ma ta shi a ruga, wanda ta ƙarbo wurin wani Malami ba za ta taɓa manta irin wahalar da azabar da ta sha ba, yoo hauka take ta ƙara shan wannan wahalar amma ta ɗauki alwashin sai ta ɗau mataki ankan Innaya don duk kan alamu sun nuna ba za ta bar ta ta mori arziki k**ar yadda ta ɗauki aniyyar yi ba.

Ashrap kuwa da tun da Innaya ta kwacesa ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi wanda yake riƙe da ita tun lokacin da ya yi arba da ita ya fara taku don shiga ciki, ya gotata ka ɗan ta ce.

'' Ya Ashrap kayan fa?.'' Ta furta cikin Muryar kuka.

'' Ki É—auka na ki ne ai.''

'' Ba ta isa kuwa kawo su nan!..." Innaya ta faɗa tana karɓe ledar hannun Dagori. '' Ai kin daina cin kayan nan ke ɗai ko kin ɗauka duk abun da ki ke ban da labari? Ko ciye kayan da ki ke ki na hana Salame duk ina sane da ke ina ganin ki idan su su Aimanah ba su so tun da ba wani bakon abu bane gurinsu to ita fa abokiyar tafiyar ta ki ai ya ci ita ki ba ta.''

Sai da ta share hawaye fuskantar kamin ta furta; '' Aradun Allah ban za ci tana so ba ai da ban hana ta ba.''

'' Mtsssss to wannan dai na yau haramiyar ki na tane ita da sauran 'yan uwanki.''

'' Kai! Innaya mu dai mun gode wallahi ki ba ta kayanta.'' Aimanah dake tashi kan dinning É—in ta furta.

'' To ba zan bayar ba ta zo ta kwata.'' Tana gama faɗin haka ta miƙa wa Salame da ke zaune kan kujera ita ma ɗin dai kallo take duk abun da ya faru a gaban idonta ta ɗan tsaya gargaɗa gurin ƙarɓa don tana tsoron abun da Dagori za ta iya yi ma ta.

'' Ki ƙarɓa kika tsaya kallon ta ba ni ce, na ba ki ba to duk wani hukunci idan ta isa ni za ta yi wa ba ke ba.'' Ƙarɓar ta yi tana godiya.

Da gudu Dagori ta nufi koridon da zai sadata da É—akin su tana kuka.

'' Mara kunyar ƙarya sai ki yi ba dai daku wa zan ba.''

**********

Shirye shiryen biki sun kank**a har yau saura kwana ki uku ɗauren Aure kuma yau ya ka sance ranar Kamu sai zuwa gobe su Nene za su zo, Dagori 'yar ayi tuni ta shige cikin ƙawayen amarya Maamah ida ake duk wani shirin biki da ita don ita fa ba ta yarda ba, ita ma 'yan mata ce har gida a ka kira mai meke-up ta zo ta ɗanɗasawa amarya da abokanta kwalliya har da Dagori da a ka yi wa Simful meke-up wanda ba ƙaramin kyau ya yi ma ta ba, doguwar rigar yadi ce jikinta blue black in da hair ɗin ya ka san ce pink color ta yi kyau sosai don ɗaurari ba ƙaramin kyau ya yi ma ta ba.

A hankali suke taku ida s**a jero su uku gwanin sha'awa tamkar wasu 'yan uku Aimanah, Inty, sai kuma Dagori su yi kyau tamkar ka sace su ka gudu su ne a gaba sai amarya dake bayan to ni idon mutane ya dawo kan su don ba ƙaramin burgewa mutane wurin s**a yi ba, barin ma mutunniyar da ta ji an saki kiɗa ta fara rawa a hankali, don tun da a ka gama ma ta kwalliya ta dubi kanta a mirro take mamakin, an ya ita ce kuwa tuni ta aro wata nutsuwa ta ɗorawa kanta don ta ɗau alƙawarin ba za ta bari a raina ta ba, ba komai ya sa ta shigewa ƙawayen Maamah ta ga sune 'yan mata kuma ta san dole idon samari zaifi raja'a ne akan su kuma ita ta tsani tana guri ace idon jama'a bai kanta, to ta lura suna da wani jin kai da ɗagawa yoo an ce idan ka shiga gari katadda kowa da binɗi to ka samu tsumma ka ɗaura dan ka zamo daidai da su.

To amma fa mutunniyar taku kun san ta akan giɗa tuni ta ware ta shiga tirƙar rawa, to ba wata rawa gayu ta iya ba ta su dai ce ta fulani, ta burge da yawan mutane gurin nan aka shiga yi ma ta barin kuɗi wasu irin yadda take faman karkaɗa kugunta da ko tudun mazaunai babu sai ƙirjin da k**ar an ɗaurawa alo zani, shi ne ke ba su dariya.

Ganin da ta yi duk uban kuɗin da ake watsa ma ta yaron MC ne ke kwashewa ya sa ta yi saurin riƙe ma sa hannu cikin ƙarar waƙa da ba jinta yake sosai ba ta ce; " Kai! Wai kai mikake nufi ne? Na ga sai kwashe min kuɗi kake da farko na ɗauka taimaka min za ka yi, tun da ni gani nan ina kwasar rawa sai na lura kai ɗin ɓarawo ne, to Aradu ka fitomin da kuɗina ko yanzu na yi ma abun da ba ka taɓa zato ba.''

Tsaye ya yi yana dubanta cikin mamaki yarinya ƙarama sai saurin ido da ƙarfin halin.

Ganin hayaniyar da ake ya sa MC kashe ƙidan. '' Wai mike faruwa ne?." Ya tambaya yana duban yaronsa ko kan yaron ya yi magana caraf, Dagori ta ce.

'' Yawwa mai hankali wannan ɗan rainin wayo ke son raina min hankali ta ya mutane suna watsan kuɗi, shi kuma ya zo yana wani kwashewa sai ka ce na sa shi ta ya ai wannan shi ne kura da shan bugu garɗi da kwasan gara to ba za ta saɓu ba Aradun Allah ba zai yiwu ba in gama ɗikar uwar rawa wani can ya zo ya kwashe kuɗi, to ka sa shi ya gaggauta aiwatar da abun da na ce ya dawo da kuɗin nan ko yanzu abun da bai da daɗi ya faru.''

Duka Mutane gurin hankalinsu ya komai kai wasu dariya ma ta ba su ganin yadda ta haƙiƙance a kai, wasu kuwa mamakin wauta irin ta,ta suke.

Maamah da haushin da Dagori ta ba tana ganin ta kunyatata gaban ƙawaye da 'yan uwan mijinta ya riƙiɗa ya koma tsoro, tsoranta kada aljanun Dagori su tashi ita kuwa ya za ta yi da su?.

Kamal da shigowarsa kenan ya wango ta da farko ma bai wayeta ba sai da ya ɗan tsinkawo muryarta duk da ba duka ya ji ba ya fahimci meke faruwa, ƙarasowa ya yi kusa da ita yana faɗin.'' Beauty meke faruwa kuma? Waye ya taɓan ke?.''

'' Ina yini? ko dan bari a gama wannan riƙincin ma gaisa daga baya yanzu bari mugama da wannan matsalar...'' Nan ta ta barta masa abun da ke faruwa duka ta ɗora da ce wa. '' To yanzu dan Allah laifi ne dan na yi magana na ga kowa ya rufeni da ido to Aradu kurwata kur kuɗi ne kuma Aradun Allah ko sama da ƙasa za ta haɗe sai an ba ni kayana a toh.''

Dariya ya yi sosai. '' Beauty rigima yanzu dama akan wannan duk kika tada hankalin ki kika hana mutane saƙet? To shi ke nan ba dai kuɗi ba to ni zan ba ki duka kuɗin da aka watsa miki kin ji ko?." Washe baki ta yi.

'' Amma fa kuÉ—in da yawa fa don Aradun Allah za su iya kai wa dubu uku.''

Nan fa mutane s**a ce mi za su yi ba dariya ba to ko mutun É—aya ya watsa ma ta sun fi dubu ashirin amma duk wannan jidalin wai akan 3k take yinsa.

'' To shi ke nan na ji zan biya har ma da ƙari.'' Da dabara ya janyeta s**a koma gurin da aka tana da don zama s**a zauna.

Nan ka shiga gabatar da abun da ya tara mutane sam ya miƙe ya fita don ya ɗaga waya ya ɗauka amma hayaniya ta hanasa ya ji sai ya fita.

Dagori da ta ga an ɗau lokaci bai dawo ba nan fa ta sa aranta ''Anya ba guduwa ya yi ba, ya hanani karɓar hakkina shi kuma da zai ba ni ya gudu.'' Ta furta a fili samm ta miƙe tana bin bayansa, a harabar hall ɗin ta shiga ba za idanu amma samm ba Kamal babu mafarinsa.

'' Lallai yau an nunamin halin 'yan birni wato guduwa ya yi da hakkina akansa? To Aradu sai ya biya don ba zan taɓa yarda ba.'' Jin motsin mutun bayanta ya sa ta waigo da niyyar magana amma sai mi ta ci karo da ƙaton mutun gabanta.

'' Waye kai? Mi....'' Ba ta samu damar ƙarasawa ba sak**akon wani Handkerchief da ya sha ƙa ma ta. '' Kai way....'' Sai ta yi lumm tana shirin faɗuwa ya tarota.

ÆŠaukar amarya ya yi ma ta cak, ya buÉ—e mulfin mota ya sa ta gidan baya ya kwantar da ita, ya koma ya shiga ya jah mutar tare da marin hall gabaÉ—aya........

Comments
Like
Share
Sune ƙwarin gwiwa ta 💪

Taku dai har kullum
MRS AWWAL 💞

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Kano
Kano