Prince24

Prince24

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Prince24, Media/News Company, Getso Bakin Kasuwa Gwarzo LG Along Karaye Road, Kano.

Photos from Prince24's post 07/02/2023

Fitacciyar jarumar wasan Hausa Maryam Wazeery (Lailai) a Shirin Labarina, ta haihu inda aka raɗawa ɗiyar nata da suna Fadeela.

Photos from Prince24's post 15/12/2021

ALHAMDULILLAHI: Addinin Musulmci Ya samu Karuwa

Mutane (104) sun Karbi Kalmar shahada a wani Gari mai suna Ijaw Dake cikin Jihar Dalta Bayan sun Karbi Addinin Musulmci sun Gudanar da Sallah Azhar Jim Kadan Bayan shigowar su

Allah Ubagiji Yasa sun shigowa Kenan

Jaridar Prince24
15/12/2021

10/12/2021

Kullum sai an kashe mutane a Arewacin Nijeriya -- Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmin Nijeriya, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar na 3 ya koka da cewa babu wata rana da ba za a kashe al'umma a Arewacin Nijeriya ba.

Sarkin Musulmin kuma ya shawarci ƴan Nijeriya da su haɗa kansu don kawo karshen ta’addanci a ƙasar.

A lokacin da yake tsokaci kan matsalar tsaro a Nijeriya a taron Majalisar Haɗin kan Addinai, NIREC, Sultan ya ce ba lokaci ba ne da mabiya addinai, musamman Musulmi da Kirista za su riƙa zargin juna da yi wa juna barazana ba.

Sarkin Musulmin ya nuna damuwa kan yadda kashe-kashe da sace-sacen jama’a ke ci gaba da afkuwa, amma kuma Musulmi da Kirista sun ɓige da nuna wa juna yatsa da yi wa juna barazana.

” Dole ne mu daina zargin juna kuma mu haɗa kai matsawar muna son mu yaki makiyanmu. Idan na ce zan yi magana kan rashin tsaro a arewa babu lokacin da za mu bar ɗakin taron nan. In ji Sultan.

Yakara da cewa , “yan kwanakin da s**a wuce mun karanta a jaridu yadda aka kona matafiya a bas a Sokoto. Babu ranar da za ta zo ta wuce ba a kashe mutane a Arewa ba, musamman Arewa maso Yamma.”

Bugu-da-ƙari Sultan ya buƙaci shugabanni da sauran hukumomin tsaro su haɗa kai su kuma fahimci girman matsalar tare da magance ta.

“Kar mu yaudari kanmu, abubuwa ba sa tafiya yadda yak**ata a Nijeriya. Na sha faɗa a lokuta da dama cewa abubuwa ba sa tafiya yadda ya k**ata. Kuma idan dai kasan matsalarka, magance ta ba zai yi maka wahala ba. Saboda haka ya k**ata mu san na yi kafin lokaci ya kure mana

08/12/2021

Ilimin Addinin Musulunci Ka Ke Buƙata Ba Boko Ba, Tsohon Kwamishina aiyuka Ya Faɗa Wa Ganduje....

Injiniya Muazu Magaji, tsohon kwamishinan ayyukan jihar Kano, ya shawarci gwamna Abdullahi Umar Ganduje .

Bisa shawarar Magaji, k**ata ya yi Ganduje ya bazama neman ilimin addini ba ya garzaya Jami’ar Harvard ba, don neman karin ilimi .

Dama an samu bayanai akan yadda Ganduje ya bazama jami’ar da ke Amurka don halartar taro akan ilimin ingantaccen shugabanci na mako guda.

Injiniya Muazu Magaji, tsohon Kwamishinan Ayyuka na jihar Kano, ya shawarci Gwamna Abdullahi Umar Ganduje akan komawa don karo ilimin addini maimakon tafiya jami’ar Harvard don karo ilimi.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Ganduje ya tafi Amurka don halartar wani taro kwas na sati daya “Bunkasa Shugabanci ” a Jami’ar Harvard da ke Boston.

Bayan samun wannan labarain ne tsohon kwamishinan ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya ba gwamnan shawara, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa, gwamnan ya fi bukatar ilimin “Makarantar Allo” ma’ana ilimin addinin musulunci.

A cewar Magaji ilimomin bokon da Ganduje ya tara sun ishe shi Magaji ya kwatanta horarwa akan ci gaban mulkin da Ganduje ya tafi Amurka don yi a matsayin abu mara amfani, ya ce digiri na farkon da ya yi a ABU da digirin digirgir din da ya yi a Ibadan sun ishe shi.

“Abinda ka fi bukata ne ba ka mayar da hankalinka a kai,” k**ar yadda ya wallafa. A cewarsa: “Makarantar Allo ka fi bukata don sanin yadda za ka gudanar ayyuka da kuma tattala dukiyar al’umma, ya k**ata ka je don ka fahimci irin hadimai na kwarai da zaka dora don kulawa da fannoni daban-daban.

08/12/2021

Mu gogaggun yan siyasa ne, ba a bakin t**i muna tsinci siyasa ba -- Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa ya dauki tsawon shekaru sama da 40 yana cikin harkokin siyasa, bugu da kari ma ita ya karanta a jami'a kuma yanzu ma ita yake yi, saboda haka ya goge a cikinta, yasan yadda ake samun rarrabuwar kai a siyasa, wanda ba sabon abu bane, kuma azo a daidaita ma ba sabon abu bane, domin ba'a daukar mutum a matsayin makiyi na din-din-din, sai dai ma ace amini na har abada.

Nasara Radio (Amanar Talaka) ta rawaito cewa, gwamna Ganduje ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da sashen Hausa na Rediyo Faransa, biyo bayan rikicin cikin gida da ta mamaye jam'iyyarsu ta APC a jihar Kano, tsakanin tsaginsa da kuma tsagin tsohon gwamna, Sanata Malam Ibrahim Shekarau, wanda har ta kai ga wata kotu a Abuja ta rushe zaben mazabu na tsagin Ganduje, ta kuma tabbatar da shugabancin tsagin Shekarau karkashin Ahmadu Haruna Dan Zago, hukuncin da tsagin Shekarau s**a ce yayi awon gaba da kujerar tsohon shugaban jam'iyyar, Alhaji Abdullahi Abbas.

Ganduje yace ana nan ana sasantawa, kuma tuni uwar jam'iyyar APC ta kasa ta shiga maganar, yace suna fatan hakonsu zai cimma ruwa, domin ita siyasa tana bukatar hakuri, idan an samu sabani to sai kuma azo a shirya, a cewarsa. Sai dai kuma wasu na ganin kalaman magoya baya na kara kunna wutar rikicin, k**ar a baya bayan nan anji muryar shugaban karamar hukumar Ungoggo, Injiniya Garba Ramat, yayi kausasan kalaman akan tsohon gwamna Shekarau da sauran yan tawagarsu.

Ya kuka kalli wannan batu?

Nasara Radio 98.5 FM
8/12/2021

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address


Getso Bakin Kasuwa Gwarzo LG Along Karaye Road
Kano