VR Hausa
Voice Radio Hausa gidan Radio ne wanda zai yinga kawo muku shirye-shirye da labaran duniya na yau da kullum
10/08/2023
Abdallah wani matashi ne Dan shekara 17 a rayuwa yana rubuta jarabawar kammala sakandare (SSCE) a lokacin da wani abin takaici ya faru wanda yayi sanadiyyar mutuwarsa
An tuhumi matashin da laifin satar waya (iPhone 7) mallakin makwabcin su Shuaibu Wambai Zumo, a staff of the Adamawa State Scholarship Board.
Wadan su mutane da aka bayyana sunan su da (operation farauta) s**a dauke Yaron daga gidansu s**a shaidawa iyalansa cewa suna son yi masa tambayoyi ne kawai.
Daga baya andawo da Abdullah gida yana kuka bayan an daure shi da mari anyi masa duka
Abdallah ya ansa laifin da ake tuhumarsa dashi inda ya shaida wa baban sa ya ansa laifin ne saboda ya tsira da ransa duba da irin azabtarwar da suke masa
Gungun mutanen da ake kira da (operation farauta) sun shigo gidan s**a nemi wayar amma basu same ta ba
Ana cikin bincike Abdallah ya fara amai jin ya fadi
Makwabcin yace babu wani abu da ya faru da Abdallah kawai yana kame kame ne Amma iyayen s**a garzaya da yaron assibitin koyarwa na jami’ar Modibbo Adama yayi kwana hudu a sume kuma ya rasu a safiyar yau (9 ga watan august 2023)
Daga baya aka gano wayar wani ne ya dauka ba Abdallah ba
Masu laifi na kokarin a rufe shari’a
Mukuma Muna neman ayiwa Abdallah adalci
06/08/2023
Shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce wasu 'yan ba-ni-na-iya ne s**a bayar da sunan Maryam Shetty don naɗa ta minista daga Kano, ba tare da saninsa ba.
Sai dai, ya ce shugaban ƙasa yana da damar naɗa mutanen da yake son tafiya da su a muƙaman ministoci daga jihohin ƙasar bisa la'akari da tsare-tsarensa da ƙwarewar mutanen da kuma sauran buƙatu.
A wata hira da ya yi da wasu kafofin yaɗa labarai ciki har da Freedom Radio ranar Asabar, tsohon gwamnan, wanda shi ne jagoran jam'iyyar a Kano, ya ce ba shi da cikakkiyar masaniya a kan Maryam Shetty, hasali ma ba su santa ba a matsayinsu na jagororin APC daga Kano.
Don haka ''ka ga ba mu da wani ma'auni da za mu ce za ta iya, ko ba za ta iya wannan aiki ba idan aka nemi shawararmu''.
Ganduje ya ce martanin da mutane s**a yi ta bayyanawa a shafukan sada zumunta, shi ma ya taka rawa wajen ɗaukar matakin sauya sunan Dakta Maryam Shetty, bayan wasu sun riƙa nuna cewa ba za ta iya riƙe muƙamin minista a Najeriya ba kasancewar ba ta taɓa riƙe wani muƙamin gwamnati ba.
Shugaban na APC ya ce da haka ne labari ya je har wajen shugaban ƙasa, wanda ya kira Ganduje don jin shawararsa.
''Ya ce min ga fa abin da ke faruwa, shin kai ka bayar da sunanta? Sai na ce masa a'a sam sam, ba ni ba ne, ban ma sani ba, daga nan ya ce to ya ka gani? akwai buƙatar a canja?, sai na ce masa ƙwarai da gaske kuwa'', in ji tsohon gwamnan na Kano.
Ganduje ya ce muƙamin minista, matsayi ne da ke buƙatar dattaku da sani (ƙwarewa), sannan yana buƙatar taka muhimmiyar rawa wajen kafa gwamnati a siyasance.
''To idan ka auna waɗannan abubuwa kuwa, ai mu ya kamata a tambaya, in dai ana so a bayar da wakilci daga jihar Kano'', in ji shi.
Ya ce ko da wani can ya bayar da wata shawara, to ya kamata a tuntuɓe su , idan ya dace sai su ba da goyon baya.
Cire sunan Maryam Shetty daga jerin ministocin Shugaba Tinubu, kamar bayyana sunanta a cikin waɗanda za a naɗa tun farko, ya yi matuƙar janyo muhawara musamman a tsakanin matasa.
Mahmoud Adam
05/08/2023
CIKIYA! CIKIYA! CIKIYA!
Jama'a, Assalamu Alaikum.
Wannan yara da kuke gani an tsince su ne jiya da daddare a guraren hanyar shiga Unguwar Rimi, ta bayan gidan man A.A. Rano dake nan cikin garin Jos.
Babbar ta ce sunan ta Nana, ƙaramar kuma Islam, sannan shi kuma yaron da ke hannun su sunan shi Nasiru.
Nana ta ce sun taho da maman su ne daga jihar Jigawa, sannan maman tace wai za su je suna a ZUNTU.
Mutanen yankin sun ce tun misalin ƙarfe 9 na daren jiya Juma'a, 4 ga watan Agustan 2023 a ka ga yaran a zaune. To amma bawan Allahn da ya haɗa mu da su, wanda kuma gidan shi na kusa da gurin da aka ajiye yaran ya ce mana mai gadin gidan man A.A. Rano ya kira shi ne da misalin ƙarfe 11 na dare don sanar da shi halin da ake ciki.
Nana dai ta ce maman su ce ta ajiye su a gurin wai su jira ta, za ta je ta siyo mu su biredi tun da yamma.
A saboda haka mu ke rokon don girman Allah, al'umma su yita yaɗa wannan rubutu da hoto ko Allah zai sa ƴan uwan su zasu gani.
Ku tuna, shi dai “YARO NA KOWA NE".
ALLAH YA BAYYANA MANA ƳAN UWAN WANNAN YARA. AMIN THUMMA AMIN.
Za ku iya tuntubar lambobin waya kamar haka domin neman ƙarin bayani akan inda yaran su ke:
Haruna Umar (07062579831)
Ibrahim Idris Badamasi (08031866089)
Baban Jos (09163994346)
Haruna Umar, Ibrahim Idris Badamasi, Unity FM/TV, Jos.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Website
Address
Kano