Government Secondary School, Rijiyar Zaki

Government Secondary School, Rijiyar Zaki

Share

School activities

14/05/2020

MASU BARCI A FARKA!!!!!

Daga:
Comrd Shafii Ibrahim Idris

Matasa a kasar Nigeria dayawa sun cancanci Kalmar nan ta cima zaune, kawai dai abin takaici shine maganar tafito ne daga inda bai kamata ba.
Amma gaskiya matasan Nigeria musamman na Jihohin Arewa yakamata mu farka daga dogon barcin da mukeyi domin idan ba hakaba saidai muji anayi a makobta. A kullum akwai abubuwan da suke bani mamaki, Haushi, takaici gamida Bashin rai dangane da matasanmu na Nigeria musamman na Arewa.

Yana daga cikin abinda yake bani Takaici shine Babban abin takaicina shine kaga matashi dan talaka Wanda wanima agidan haya mahaifinsa yake kuma matashin mai shekara ashirin da biyar koma sama da haka Amma baisan komai ba sai Swagger, Zuwa gidan kallo da filin kwallo. Gaskiya wannan babban abin takaici ne. Musamman idan akayi LA akari da wannan rayuwar da kuma yadda salon zalunci yake karuwa acikin shugabanni.

Yakamata ace da Wanda yayi karatu mai zurfi da Wanda baiyiba kowanne ya tashi ya nemi MAFITA arayuwa kada ka hada kanka da Dan wani mai kudi ko Dan siyasa na UNGUWA da kaga yana irin wannan. Abinda Baku saniba shine. Wannan baban NASA yana nan yana tsara masa rayuwarsa tagaba. Kuda kuke biye masa ana nan ana nan zakuga wataran kawai ankaishi wani guri ko anbashi wani aiki daganan sai yamaida Ku almajiransa ko bayinsa. A maimakon haka yakamata matasanmu su sani rayuwar Samartaka ba rayuwar jin dadi da morewa bace kawai. A a. Rayuwace da tafi kowacce rayuwa daraja da amfani sannan itace rayuwarda tafi kowacce hatsari domin kuwa muddin kayi sake ko wasa da ita zakayi danasani.
Rayuwar samartaka yaku yan'uwa matasa itace rayuwar da ake Gina rayuwar gaba (Building future life) sannan itace Wanda idan kayi sake zaka lalata rayuwarka ta gaba (destroying future life ).
Dan haka yakamata matasa su sani cewa raina karamar Sana'a banasu bane domin Sana'a albarka gareta. Kada mu dogara ga gwamnati domin yanzu shugabanni ba tamu sukeba. Yakamata muyi yunkurin gyara rayuwar

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Address


Kano