Jaridar Hausa Reporters
... Inganci
30/12/2025
Hon. Bello Aminu B/Ruga, tsohon Mataimakin Shugaban Riko na Gudanarwa na Karamar Hukumar Makoda, ya bayyana matsayinsa tare da Shugabansa da kuma caucus ɗinsu na siyasa, inda s**a jaddada tsayuwarsu daram tare da Jagora Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, Shugaban jagoran Jam’iyyar NNPP na kasa.
A cewarsa, wannan matsaya ta samo asali ne daga gamsuwa da hikima, hangen nesa, da falsafar siyasar Jagoran, wanda ke tafiyar da siyasa bisa adalci da kishin al’umma. Ya ƙara da cewa, su ba za su taɓa cin amanar tafiyar Jagora Kwankwaso ba ko ta wace hanya.
Rahoton ya kuma nuna cewa sun yi addu’ar Allah Ya ci gaba da ba Jagoran jagoranci, hikima, da kariya a dukkan al’amuransa na siyasa da rayuwa.
30/12/2025
30/12/2025
Hon. Umar Aliyu Burji, tsohon Interim Vice Chairman na Karamar Hukumar Doguwa kuma Shugaban Ƙungiyar Mataimakan Riko na Kano ta Kudu, ya bayyana goyon bayansa ga Jagora, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, yana mai jaddada cewa wannan matsaya ta fito ne daga zuciya ɗaya da fahimta ta gaskiya.
Ya bayyana hakan ne tare da Shugaban Caucus ɗinsa na Doguwa, Hon. Ukasha Adam Ririwai, inda ya ce ya gamsu ƙwarai da adalcinsu, hangen nesansu, da kuma yadda suke tafiyar da harkokin siyasa cikin gaskiya, rikon amana, da bin doka.
Tare da fatan cewa za a ci gaba da tafiya a wannan tafarki domin amfanin jama’a da ci gaban Kano ta Kudu da Najeriya baki ɗaya.
30/12/2025
05/09/2025
Jagoran da ya k**ata ya zama kariya ga jama’a ya juya ya zama barazana garesu; Shin a haka zamu cigaba da rayuwa?
By Yakub Nasir Khalid
Mutum mai iyali da yara sama da ashirin, amma bai iya tsayawa wajen kare ‘ya’yan al’ummarsa daga yunwa, rashin ilimi, damuwa da lafiyarsu da rashin aikin yi. Tunda ya kasa kare jama’arsa daga wulakanci da samar da abin da ya dace, shin mai yasa ya tsaya tsayin daka wajen kare kansa daga zarge-zargen kisa......?
Jagoran da ya k**ata ya zama kariya ga jama’a ya juya ya zama barazana gare su. Lokacin da ake buƙatar kulawa da ci gaba, ya jefa jama’arsa cikin damuwa da far aba musamman lokutan zabe. Lokacin da ake bukatar shugabanci da adalc, hakan ya tabbatar da cewa shi ba jagora na gari bane.
An zarge shi akan abubuwa da dama da ya k**a ta amasa hukunci akan domin kare alumma daga koma bayan tarbiyya da kuma samun ingantaccen Shugaban a yankin, amma ya Shiga rigar mulki ya buya.
A shekarar 2023 akwai tarin zarge-zargen kisa, kone gidaje, da jefa jama’a cikin rikici sun tabbatar da cewa siyasar sa bata kawo ci gaba ko zaman lafiya bace, illa tashin hankali da rugujewar al’umma yankinmu. Wanda hakan kawo rasa rayuwakan mutane da dama, shin a haka zamu cigaba da rayuwa?
Alhassan ba jagora ba ne, bala’i ne ga jama’a. An zarge shi da kisan kai, tashin hankali da kone ofis, abin kunya da wulakanci. Shugabancinsa kazanta ne da ke rusa alumma, mutum mai irin wannan tabo bai cancanci kujerar jama’a ba.
A 2023 ya shiga hannun jami’an tsaro bisa zargin kisan kai da haɗin baki wajen tada rikici a Tudun Wada. Shugaba na gaskiya da kuma son cigaban alumma bazai bai k**ata a taɓa danganta shi da jinin al’ummarsa ba; tabbas muna bukatar sauyi.
A lokacin yaƙin neman zaɓe a 2022, Doguwa ya ce a fili: “Ranar zabe ko dai ku zabi jam’iyyar APC, ko kuma a yi muku hukunci.” Wannan magana ba siyasa ba ce, barazana ce ga jama’a. Shugaban da ke barazanar jama’arsa ba shugaba ba ne, mai zalunci ne.
Yakub Nasir Khalid
Email: yakubunasirukhalid@gmail
YANZU-YANZU: Gwamnan jihar Niger, ya sauke dukkanin kwamishinoninsa.
08/07/2025
Ba za a sanar da wajen casun shagalin bikin cikar Lamine Yamal shekaru 18 a duniya ba, sai ana sauran kwana biyu shagalin bikin. Kuma za a sanarwa waɗanda zasu halarci wajen ne kawai inda za a yi taron.
Sannan kuma matashin ɗan wasan na Barcelona, ya sanya dokar hana shiga da waya wajen casun shagalin bikin na shi.
Daga Fagen Wasanni
08/07/2025
Noma: Babban Malamin addinin Musulunci, kuma shugaban majalisar malamai na ƙungiyar Izala a gonar shi dake Jingre, ƙaramar hukumar Bassa dake jihar Filato.
Shin akwai abin koyi a cikin hakan kuwa?
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Kano