Ibrahim muhammad

Ibrahim muhammad

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Ibrahim muhammad, Public Figure, Kano.

22/10/2025

Wata rana za a kira sunanka, amma ba za ka iya amsawa ba.
Za a zo gidanka, amma ba don ziyara ba — sai don ɗaukar gawarka.
Za a ɗora ka kan abin da ba ka taɓa hawa ba — tabarmi mai sanyi.
Za a lullube ka da farin zani, ba kayan alfarma ba.
Za a binne ka cikin ƙasa, wacce ka taɓa takewa da ƙafafunka.

Duniya za ta ci gaba kamar baka taɓa wanzuwa ba.
Mutane za su yi kuka, amma daga baya su manta.
Abin da ka tara, wani ne zai mallaka.
Abin da ka so, zai zama tarihi.
Sai abin da ka aikata da niyyar Allah shi kaɗai zai zama rakiyarka.

Ka tsaya ka tambayi kanka,
🕯️ Idan yau ne lokacin nawa, na shirya kuwa?

27/09/2025

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

Babban Malaminmu Sheikh Lawan Abubakar Shu'aib Triumph Zai dawo dukkan wasu Karatuttuka da ake gabatarwa.

Yau ma Akwai karatun littafin "Allu'u lu'u wal Marjan" da ake gabatarwa duk Asabar. 27 Sep 2025.

Muna Addu'ar Allah yaba malam kariya Allah ya ƙarfafeshi.

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Kano