Hausa Channel
TARIHI DA AL-ADUN ƘASAR HAUSA
04/04/2026
JIYA BA YAU BA
Alhaji Yusuf Maitama SuleAbout this soundYusuf Maitama Sule (Taimako·bayani), Ɗan Masanin Kano An haifi Maitama a Shekarar alif dari tara da ashirin da Tara (1929), a unguwar Yola, cikin garin Kano. Maitama shi ne na uku a jerin ‘ya’ya a gidansu, sauran yan'uwa biyu mata ne; wato, Rabi, wacce ake kira Yaya ta Zagi, Maimuna wacce ake kira Yaya ta Bichi.
An sa masa suna Yusuf, saboda sunan Mahaifin Madakin Kano Mahmudu, shi Madaki yana kiran shi Abbana. Sunan Maitama kuwa an sa masa shi ne saboda Galadiman Kano Yusuf, saboda an yi amfani da mak**ai sosai lokacin basasar Kano. Akan yi wa duk wani mai suna Yusuf laƙabin Maitama.
Madakin Kano ya yi wa Mahaifin Maitama, Abba Sule Danmuri, mai kula da dukkan al’amuransa na gida da kula da Dawakai. Maitama, yana dan shekaru 4 mahaifiyarsa Hauwa, wacce ake kira ‘Yarkayi ta rasu. Ita ALLAH ya yi ta ne mace mai ban dariya, mai raha, ba ta fushi, shi ya sa duk bikin da ya tashi ita ake kira ta yi ta magana a gidan bikin, halinta da iya maganarta Maitama ya gado
A shekarar 1943 Maitama ya shiga kwalejin Kaduna, yana dan shekaru 13. Maitama, ya kammala karatunsa na kwaleji cikin shekarar 1948, ya kuma k**a aikin Malanta, a makarantar Middle ta Kano.
Maitama sun tsaya zabe da shi da tsohon Malaminsa a makaranta, Malam Aminu Kano, wannan zabe ya gudana ne a Central Office, wannan abu ya faru ne cikin shekara ta 1954.
Ya Rasu a Kairo, 3 ga Yuli, 2017 Muna fatan Allah ya yi masa Rahama kuma yagafarta masa, ya kuma sa aljanna tazama makomarsa
Waiwaye..
Al-ummar Musulmi Kenan a Wata Ranar Jumma'ar Shekarar 1959 yayin gabatar da Sallar Jumma'a a Babban Masallacin Birnin Kano. Shekaru sittin da Bakwai (67) Kenan da s**a Gabata.
Allah ya jikan Magabatanmu
26/02/2026
Gamji Uban Yan Boko Sir Ahmadu Bello Sardauna.
*Ya gina Bankin Arewa -
*Ya gina A.B.U Zaria,
* Ya gina Polytechnic a Kaduna.
* Ya gina gidan rediyon Najeriya a Kaduna
*Ya gina Cibiyar Nazarin Dabbobi a Vom, -
*Ya gina Arewacin Najeriya - Investments Ltd (NNIL).
*Ya gina filin wasa na Ahmadu Bello mai kujeru 16,000, Kaduna -
* Ya gina Kwalejin Aikin Noma a Yandev. -
* Ya gina Makarantar koyon aikin jinya a Malumfashi. -
* Ya gina Kwalejin Larabci a Kano. -
* Ya gina makarantar horas da sojoji ta Najeriya a Kaduna. -
*Ya gina Makarantar Soja a Zariya.
* Ya Gina Arewacin Najeriya - Kamfanin Raya Kasa A Kaduna,
*Ya Gina Defence Industrial Corporation a Kaduna
*Ya gina jaridun New Nigeria a Kaduna
* Ya gina kamfanin buga littattafai na Arewacin Najeriya a Zariya
* Ya gina kamfanin ci gaban Arewacin Najeriya (NNDC).
Allah ya kyautata makwanci
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Telephone
Website
Address
Kofar Nassarawa
Kano