DAN KASA
Public reporter's jarida ce cikin harshen Hausa wacce ke kawomuku ingantattun labarai na duniya da g
22/02/2025
SANARWA ZUWA GA MASU NEMAN SHIGA AIKIN 'YAN SANDA
Hukumar kula da aikin 'yan sanda na Kasa
(POLICE SERVICE COMMISSION) karkashin jagorancin DIG Hashimu Argungu (mai ritaya), tare da hadin gwiwar rundinar 'yan sandan Nigeria karkashin jagorancin IGP Kayode zasu debi sabbin kuratan 'yan sanda
K**ar yadda sanarwa yazo, wannan karon babu batun cike takardan neman shiga aikin 'yan sanda saboda karancin lokaci, za'a deba ne daga cikin wadanda s**a taba neman shiga aikin har s**a rubuta jarabawa na Computer Based Tests (CBT) a ranar 5 da 6 na watan March shekarar 2024 amma basu kai ga nasaran samun aikin ba, to daga cikinsu za'a diba
A yanzu ana bukatar su shiga cikin wannan website din da za'a bude zuwa nan da karfe 12 na ranar yau👇
https://apply.policerecruitment.gov.ng
Wanda ya ga sunansa sai yayi printing invitation slip zuwa gurin da za'ayi gwajin lafiya wato medical screening a Police Hospitals dake Zonal Headquarters guda 17 a fadin tarayyar Nigeria
Za'a fara medical screening nan da kwanaki hudu wato ranar 26-2-2025 sannan a kammala zuwa ranar 12-3-2025, wanda bai samu yayi ba shikenan ya wuce shi
Ku taimaka wajen isar da wannan sakon saboda ya isa ga 'yan uwa musamman na kauyuka
Allah Ya bawa mai rabo sa'a
26/10/2024
An daka wa motar Taliya wawa a Kaduna.
Mutane sun daka wa wata babbar mota maƙare da taliya wawa, bayan da ta faɗi kusa da gadar sama ta Sabon Tasha da ke Jihar Kaduna.
22/02/2023
Zaɓe: A kasa, a tsare, a raka ba zai yi aiki ba wannan karon, in ji INEC
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC ta ce tsarin a kasa a tsare, a raka ba zai yi aiki ba a zaɓen bana.
INEC ta shaida hakan ne a wata tattaunawa da BBC ta yi da jami'arta, a ci gaba da kawo bayanai kan muhimmancin abubuwa da ya kamata a sani ko tunatarwa kafin ranar zaɓe.
Hukumar INEC ta ce a yanzu sai dai a ce a kasa a tsare a rumfar zaɓe, saboda komai zai kasance cikin na'ura wanda za a riƙa aikewa kai-tsaye zuwa cibiyar tattara sakamako.
Hajiya Zainab Aminu Abubakar da ke magana da yawun hukumar ta ce ta yanar gizo za a rinƙa aike sakamakon zaɓen.
Shugaba Muhammadu Buhari ya qara wa’adin naira dari biyu da taci gaba the anfani har zuwa kwana sittin daga jiya. Saboda haka jamaa Sai muyi hakuri, mubi doka, mucigaba da al’amuran mu cikin lumana. Allah Ya taimake mu. Ameen.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Telephone
Address
Kano