Arewa Pulse

Arewa Pulse

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Arewa Pulse, News & Media Website, Yola, Adamawa, Kano.

07/05/2026

Da Yuwuwar Gwamna Umaru Fintiri Ya Ayyana Abdulrahman Bashir Haske A Matsayin Magajinsa A 2027

Ana ci gaba da samun bayanai daga majiyoyi daban-daban da ke nuna cewa, akwai yiwuwar Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri zai bayyana sunan Abdulrahman Bashir Haske a matsayin wanda yake so ya gaje shi a takarar gwamnan jihar a zaben shekarar 2027.

Rahotanni daga cikin masu ruwa da tsaki a harkar siyasar jihar sun nuna cewa, ana gudanar da tattaunawa mai zurfi tsakanin manyan jiga-jigan jam’iyya domin ganin an cimma matsaya ta hadin kai kafin fara yakin neman zabe.

Masu bibiyar siyasar Adamawa na ganin cewa Abdulrahman Bashir Haske na kara samun karbuwa a tsakanin matasa, masu sana’o’i da kuma wasu manyan masu fada a ji a jihar. Hakan ne yasa ake ganin sunansa ya fara fitowa sosai a matsayin wanda zai iya daukar tutar jam’iyya a zaben da ke tafe.

Wasu na kallon wannan mataki a matsayin salon siyasar “consensus” wato tsarin da shugabannin jam’iyya ke zama su amince kan mutum guda domin kaucewa rikici da rabuwar kai tsakanin ‘yan takara. Wannan tsari dai ya saba bayyana a manyan jam’iyyun Najeriya musamman idan lokacin zabe ya karato.

Duk da cewa har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga bakin gwamnan ko shugabannin jam’iyya, amma masu sharhi kan siyasa na cewa alamomi na nuna akwai yiwuwar a bayyana Abdulrahman Bashir Haske a matsayin zabin da ake so ya jagoranci tafiyar siyasar jihar a nan gaba.

Haka kuma, wasu magoya bayan siyasa a Adamawa sun fara bayyana wannan labari a matsayin wani sabon babi da zai iya sauya yanayin siyasar jihar, musamman ganin yadda ake cewa ana neman matashi mai hangen nesa, ilimi da kuma kusanci da al’umma.

Idan har wannan batu ya tabbata, hakan na iya zama daya daga cikin manyan sauye-sauyen siyasa da za su dauki hankalin jama’a a Arewa maso Gabas gabanin babban zaben shekarar 2027.

Sai dai masana siyasa na gargadin cewa har yanzu lokaci bai yi ba na yanke hukunci kai tsaye, domin siyasar Najeriya na da sauye-sauye masu zuwa cikin kankanin lokaci. Duk da haka, maganar Abdulrahman Bashir Haske na ci gaba da yawo a bakin jama’a tare da jawo muhawara a fagen siyasar Adamawa.

Arewa Pulse Report

26/04/2026

Anga Abun Al’ajabi a Jahar Adamawa; Abdulrahman Bashir Haske Ya Bayyana Aniyarsa ta Tsayawa Takarar Gwamnan Adamawa a 2027

An shaida wani babban tarihi mai ɗaukar hankali a jihar Adamawa State bayan da Alhaji Abdulrahman Bashir Haske ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar a shekarar 2027. Wannan sanarwa ta zo ne a wani katafaren taro da aka gudanar a Mahmudu Ribadu Square, inda dubbannin jama’a daga sassa daban-daban na jihar s**a halarta domin nuna goyon baya.

Taron ya ja hankalin jama’a da dama, inda aka ga mutane na tururuwa suna ci gaba da shigowa wajen tun kafin fara taron. Rahotanni daga mahalarta taron sun nuna cewa an samu cunkoso da tarin jama’a daga ƙananan hukumomi daban-daban na jihar, lamarin da ya sanya wajen taron ya cika maƙil da masu goyon baya.

Alhaji Abdulrahman Bashir Haske, wanda ake kallon sa a matsayin ɗaya daga cikin matasan da s**a yi fice wajen ayyukan ci gaban al’umma, ya bayyana cewa burinsa shi ne kawo sauyi mai ma’ana ga jihar tare da samar da ci gaba a fannoni daban-daban kamar ilimi, kiwon lafiya, samar da ayyukan yi da kuma inganta rayuwar matasa.

Mutane da dama da s**a halarci taron sun bayyana cewa ba su taba ganin irin wannan taro ba a tarihin Adamawa State. Wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana cewa irin yadda jama’a s**a fito domin nuna kauna da goyon baya ga Alhaji Abdulrahman Bashir Haske ya nuna irin farin jinin da yake da shi a zukatan al’umma.

Masu sharhi kan harkokin siyasa a jihar na ganin cewa wannan mataki na bayyana aniya zai iya sauya yanayin siyasar jihar nan gaba, musamman ganin yadda matasa da kungiyoyi daban-daban s**a nuna cikakken goyon baya ga wannan yunkuri.

A yayin da ake ci gaba da tunkarar shekarar zaɓen 2027, wannan babban taro ya zama abin magana a faɗin jihar, inda mutane da dama ke bayyana shi a matsayin wani sabon babi a siyasar Adamawa State.

Arewa Pulse Report

23/04/2026

Cece-kuce ya kare; Abdulrahman Haske Zai Bayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Gwamnan Adamawa A Ranar 25 ga Afrilu

Abdulrahman Haske ya kammala dukkan shirye-shiryen da s**a dace domin bayyana aniyarsa ta shiga takarar kujerar gwamnan Jihar Adamawa a zaɓen da ke tafe, a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Wannan mataki na zuwa ne a wani lokaci da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi a faɗin jihar, yayin da masu ruwa da tsaki da magoya baya ke ci gaba da bibiyar masu neman shugabanci.

A cewar bayanan da aka samu, an shirya gudanar da babban taron bayyana wannan aniya ne a ranar 25 ga watan Afrilu, a dandalin Mahmud Ribadu Square da ke birnin Yola, babban birnin Jihar Adamawa. Ana sa ran taron zai zama ɗaya daga cikin manyan tarukan siyasa da za su ja hankalin jama’a daga sassa daban-daban na jihar.

Kungiyar MAGA dake karkashin Alhaji Abdulrahman Haske, ta bayyana cewa ana sa ran dubban mutane za su halarci wannan taro, inda ake hasashen kimanin magoya baya 100,000 za su taru domin nuna goyon baya ga wannan takara. taron zai haɗa da shugabannin jam’iyyar APC daga matakai daban-daban, manyan jiga-jigan siyasa, abokan hulɗa, ƙungiyoyin matasa da mata, da kuma sauran masu ruwa da tsaki daga ƙananan hukumomi da al’ummomin jihar baki ɗaya.

Rahotanni sun nuna cewa ana gudanar da shirye-shirye masu faɗi domin tabbatar da cewa taron ya gudana cikin tsari da nasara, tare da samar da yanayi mai kyau da zai bai wa mahalarta damar bayyana ra’ayoyinsu da goyon bayansu. Ana kuma kallon wannan taro a matsayin wani muhimmin mataki da zai iya nuna ƙarfin siyasar Abdulrahman Haske da yadda yake da farin jini a tsakanin jama’ar Adamawa.

Masu lura da al’amuran siyasa na ganin cewa bayyana wannan takara na iya ƙara ɗaukar hankalin jama’a, musamman a lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan makomar shugabanci da ci gaban jihar. Haka kuma, ana sa ran wannan taro zai zama wata dama ta haɗa magoya baya da kuma bayyana manufofi da hangen nesa ga makomar Adamawa.

Arewa Pulse Report

Photos from Arewa Pulse's post 16/04/2026

Why the People of Adamawa Are Rallying Behind Abdulrahman Bashir Haske

In Adamawa State, support for Abdulrahman Bashir Haske continues to grow as many residents link their backing to what they describe as his consistent contributions to the state’s development.

Supporters say their loyalty is also a form of appreciation for his past efforts in supporting communities and investing in initiatives that promote growth and opportunity. His decision to bring his business interests and investments into Adamawa is widely seen as a rare commitment among political aspirants.

Many believe no other candidate has shown the same level of personal involvement in developing the state. For them, Haske represents not just a political choice, but a reflection of gratitude and trust in his continued vision for Adamawa’s progress.

Signed
AB HASKE MAGA MEDIA TEAM

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address


Yola, Adamawa
Kano