Governor Abba Kabir Yusif Project Update
NEW PROJECT UPDATES, CURRENT NEWS ON THE ADMINISTRATIVE
Furucin tuzura da kawo hargitsi da cin mutunci mutane Wanda danbalki yayi yakaishi prison
HALIN DA GWAMNATIN ABBA GIDA-GIDA TA SAMU MAKARANTUN GABA SAKANDIRE...
Toh a zahirin gaskiya, mun samu makaratun gaba da sakandire cikin mawuyacin hali, munyi mamaki kwarai, yadda aka bar ilimin jihar Kano ya lalace, duba da irin gyaran da Engr Rabiu Musa Kwankwaso(PhD) yayiwa harkar kafin barinsa mulki, a shekarar 2015. Kaɗan daga cikin matsalolin da muka samu sun haɗa da:
1. Mun samu makaratun babu sabbin Gine-Gine tsawon shekaru takwas(8).
2. Babu kayan koyo da koyarwa, musamman fannin kimiyya da fasaha.
3. An dakawa filayen makarantun wawa, babu la'akari da filayen zasuyi amfani wurin faɗaɗa makarantun.
4. Makarantun wajen birni dake karkashin Polytechnic basu samu wasu aikace aikacen cigabansu ba. Su kansu ɗaliban basu da cikakken ɗakunan kwana (Hostels), ballantana ɗakunan ɗaukar darasi (Lecturer Theatres)..
5. Babu cikakkun malamai da kyakkyawan tsaro a makarantun, wasu daga ciki makarantun basu da Katangu da s**a zagaye su ba.
Dr. Yusuf Ibrahim KofarMata
Komishinan Ilimi Mai Zurfi
Kano State, Nigeria
23 January, 2024
21/01/2024
Alhamdulillah!
Nan bada jimawa ba, za' ayi bikin bada takardun shaidar kammala karatun ɗaliban jami'o'in Bells, Igbinedion dana Al'qalam, wanda s**ayi karatunsu zamanin Maigirma tsohon gwamnan jihar Kano, Engr. Sen. Rabiu Musa Kwankwaso. Bayan hawan Dr Abdullahi Umar Ganduje, anyi ta fama dashi wurin biyan sauran kuɗaɗen das**a rage, amma abun yaci tura.
Kwanakin baya muka shaida muku cewa, Maigirma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya biya sauran kuɗaɗen da s**a rage domin karɓo certificates ɗin, kuma mun nuna muku tuni sun zo hannun gwamnati. Alhamdulillah, ɗaliban sunyi hazaka sosai, domin an samu masu First Class da yawa. Harda masu Masters acikinsu. Bamu masu Third Class ko pass a cikin su ba.
Dr. Yusuf Ibrahim KofarMata
Komishinan Ilimi Mai Zurfi
Kano State, Nigeria
21 January, 2024
OYOYO ABBA KANAWA
POLICE MUNA
KANAWA
SUNA GODIYA
BY ALLIYA ABBA GIDA GIDA YKS
20/01/2024
Kamar yadda mutane suke neman sanin requirements ɗin da ake buƙata wurin samun tallafin ƙaro karatun digiri na biyu a kasashen duniya, wanda Gwamnatin jihar Kano take daukar nauyi, karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf .
Mun samu, mun zaƙulo muku su kamar haka:
1. Bsc Certificate
2. Transcript
3. Waec/Neco/Nabteb
4. Primary certificate
5. Local government indigene
6. State Indigene
7. Birth certificate
8. International passport
9. NYSC certificate
Yana da kyau ayi tanadi, domin gwamnati zata cigaba da tura ɗaliban ta masu albarka nan bada jimawa ba.
20/01/2024
RESULT ƊIN ƊALIBAN INDIA YA FITO DA CIKAKKIYAR NASARA
Ƙwalliya ta biya ƙudin sabulu, kwanaki muka sheda muku cewa ɗaliban mu masu albarka da gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf ta ɗauki nauyin karatun digiri na biyu(Masters), sunyi kuma sun kammala jarabawar zangon karatunsu na farko, wato Semester 1.
Alhamdulillah, cikin ikon Allah, sakamakonsu ya fito cikin nasara, inda mafi akasarin ɗaliban s**a dinga yiwa jabawar cin kacha. Cikin hotunan dake ƙasa, sakamakon wasu daga cikin ɗaliban ne na jami'ar Sharda da suke tsangayar Biotechnology.
Yawancin su sunci A's a kwasa-kwasai da s**a ɗauka, kuma cikinsu babu mai ƙasa da 8/10 points. Daman chan wannan shine tsammanin mu gare su, tunda duk masu First Class ne.
Allah ya cigaba da basu Nasara🤲
Yusuf Ibrahim KofarMata
Komishinan Ilimi Mai Zurfi
Kano State, Nigeria
20 January, 2024
18/01/2024
Masha Allah
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano