Taskar Alheri Media

Taskar Alheri Media

Share

Taskar Alkhairi Shafi ne da ke kawo muku sahihan labarai, sharhi da nazari kan harkokin siyasar Najeriya cikin harshen Hausa. Ku biyo mu

03/05/2026

“Muna cigaba da zurfafa tuntuba ciki harda jagororin jam’iyyun NDC,PRP da wasun su don samun zabi mafi dacewa da zai kare muradunmu na dimokradiyya”

Cewar Jagoran Darikar Kwankwasiyya

Sanata Kwankwaso, wanda jigo ne a jam'iyyar ADC, ya bayyana hakan ne bayan raɗe-raɗin da ake yi game da makomarsa a siyasa, duba da irin ƙalubalen da jam'iyyar ke fuskanta.

Ya kuma jaddada cewa har yanzu bai yanke shawara game da makomarsa da na abokan hulɗar siyasarsa ba, sai dai ya ce nan ba da jimawa ba, za su sanar da matsayarsu.

02/05/2026

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce har yanzu bai yanke hukunci na karshe kan makomarsa ta siyasa ko ta magoya bayansa ba, duk da rade-radin da ake yi kan yiwuwar sauya sheka daga jam’iyyar ADC.

A wata sanarwa da ya fitar, Kwankwaso ya ce akwai bayanai masu rudani da ke yawo a kafafen yada labarai dangane da matsayinsa a siyasa, musamman bayan matsalolin da ke addabar ADC.

Ya bayyana cewa hukuncin kotun koli da ya tabbatar da halascin kwamitin gudanarwa na kasa karkashin jagorancin David Mark ya kuma mayar da shari’ar zuwa babbar kotu, lamarin da ya sanya jam’iyyar cikin wani yanayi mai sarkakiya.

Kwankwaso ya kara da cewa wata babbar kotun tarayya ta kuma soke halascin babban taron jam’iyyar na baya-bayan nan, yayin da babban lauyan gwamnatin tarayya ya nemi wata kotu ta soke rajistar ADC.

Tsohon ministan tsaron ya ce sun fice daga jam’iyyar NNPP ne saboda matsalolin shari’a da ya ce wasu na waje s**a haddasa, yana mai cewa yanzu ADC ma tana fuskantar irin wannan matsala.

Saboda haka, ya ce shi da sauran masu ruwa da tsaki sun fara tuntubar wasu jam’iyyu da shugabanninsu ciki har da NDC da PRP domin duba mafi alherin mataki na kare muradunsu na siyasa da dimokuradiyya.

Kan batun takarar shugaban kasa kuwa, Kwankwaso ya ce bai bayyana aniyar tsayawa takara ba, kuma bai goyi bayan kowane dan takara ba. Ya tuna cewa a zaben fidda gwani na APC a 2014 ya zo na biyu bayan Muhammadu Buhari, sannan a 2019 ya nemi tikitin PDP kafin daga bisani ya mara wa Atiku Abubakar baya bayan ya lashe zaben fidda gwani.

Kwankwaso ya ce a kullum yana fifita hadin kan jam’iyya da muradun kasa sama da bukatun kansa.

Ya kuma bayyana cewa rashin halartarsa a tarukan masu ruwa da tsaki na ADC guda biyu da aka yi kwanan nan ya faru ne saboda wasu uzurori na kashin kai, kuma ya sanar da shugabannin jam’iyyar tun da wuri.

A karshe, ya ce duk wani hukunci da zai dauka game da alkiblarsa ta siyasa za a sanar da shi ne ta hanyoyin hukuma a lokacin da ya dace.

30/04/2026

Ba gaskiya ba ne labarin cewa matasa sun ƙone gidan Nafiʼu Bala a jihar Gombe.

Kakakin ƴan sandan jihar ASP Buhari Abdullahi ne ya tabbatar da hakan, Ya ce labari ne na ƙanzon kurege wasu masu son tada hankali ke yaɗawa.

Ya ƙara da cewa, unguwar da ake magana ma ba a nan Nafiʼun ya ke ba, yanki ne da iyayensa su ke, kuma babu wani abu da ya faru.

Har zuwa yanzu mazauna yankin da ake yaɗawa sun tabbatar da cewa babu gaskiya a labarin.

Kazalika an soma yaɗa hotunan ne tunda yammaci, amma kuma hotunan sun nuna lokaci ne na dare.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


Zoo Road, Kumbotso LGA
Kano
700101