Algaita dub studio

Algaita dub studio

Share

Algaita dub studio

22/08/2021

Muna da isassun masoyan da ko da yaushe fassarar mu kadai suke dako, kuma mu su muke yi wa fassara.

* Annabin Rahma yace ka fadi alheri ko kayi shuru, hakazalika a wani Hadisin yace musulmi shine wanda jama'a s**a kubuta daga "harshen sa" da "hannun sa". Saboda haka fadan maganganu yasassu ko zagin mutane ba dabi'ar musulmi bace.

* Duk wanda ya sake zagin mu a wannan shafi ko ya fada mana magana ta cin mutunci, to zamuyi "banning" nashi daga wannan shafi a matsayin shi na magaucin da ya sanya rigar masoya. Ko muyi "blocking" nashi daga sake mu'amalantar shafin mu. Amma hakan ba yana nufin kada masoya su kawo mana korafe korafen su bane, duk mai korafin sa ya kawo zamu saurare shi, zagi da cin mutunci ne baza mu dauka ba daga masu fakewa da cewa su masoya ne.

* Burin mu shine wannan shafi ya zamo tsaftataccen fage da masu hankali zasu tattauna lamuran da s**a shafi maqasudin samar da shafin cikin tsari da fahimtar juna, ba ya zama wani waje kamar tasha ba, wanda hakan yana ci wa asalin masoya na hakika tuwo a kwarya.

Muna son ku muna tare daku masoyan mu na asali 😍, magauta kuma👹, ko ku iya lafazi ko ku bar mana shafi. Mu tawagar da'a da sanin ya kamata muke, bama zagi ko cin mutunci.

A kafta!

22/08/2021

ANZO WAJEN!!!

Hallau dai sabuwar fassara mai suna "RUNDUNA" ta fita a kasuwa, na Jarumi Mahesh Babu, ku antaya kasuwa ku damalmale ku sheke kwarkwatocin idanunku.

JINJINA gareku Masoyan Algaita Dubstudio 💪🏻

To ai hikenan A kafta sharing wa Masoya! 🎬

Naku:- Mu'hd Ladan Buhari Mallam

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address


Anguwar Nasarawa
Kano