Taskar Jaridu

Taskar Jaridu

Share

Taskar Jaridu Shafin Samar da labarai Na Cikin Gida Har Da Kasashen Ketare, Kana Da Kuma Isar Da Koken Talakawa Zuwaga Shugabanni Cikin Gaggawa...

Photos from Taskar Jaridu's post 24/06/2022

Dalibai yan asalin jihar Kano sun yi tur da tofin Allah tsine ga shugaban kungiyar daliban Comr Yahya Usman Kabo bisa siyasantar da kungiyar daliban da yake yi da sunan neman kuɗi.

Daliban sun kara bayyana cewa shugaban nasu babu abinda yake yi sai son zuciya tare da nuna dalibai a matsayin kwadayayyu alhali miyarsa kawai yake wankewa da sunan dalibai.

Cikin fushi wani dalibi mai suna Muhammad Musa ya sake jaddada cewa duk abinda shugaban yake yi cin mutuncin dalibai yan asalin jihar Kano ne kuma suna Allah wadai da abinda yake yi.

Wannan duk yana biyowa ne bayan shirin da shugaban daliban yayi ma yin taron marawa APC baya a jihar Kano a ranar Lahadi mai zuwa.

Rahotan: Nigerian New's Hausa

22/06/2022

Musulmi Dan Shekara 30 Ya Auri Kirista Mai Shekaru 75 A Jamus

Daga Barista Nuraddeen Isma'eel

"Wani matashin balarabe Dan asalin kasar Iraqi mai suna Muhammad, ya auri wata tsohuwa mai shekaru 75 ita kuma haifaffiyar kasar Jamus."

"Rahoton yacigaba da bayyana cewa! Ya hadu da baturiyarne mai suna Jessica a kasarsu ta jamus bayan sharfe shekaru 7 yana zaune a kasar."

"Majiyar bai boye Mana komaiba; inda Matashi Muhammad s**a kwashe wasu lokuta masu tsayin gaske suna soyayya da juna, bisani baturiya Jessica taji Kawai burinta ta auri wannan matashi, ba'ayi wata-wataba baturiyan ta fara bude masa ido da kudi, kanama hadda bashi mota ta miliyan "350" a domin ya fattama a gari."

Daga karshe dai Muhammad ya yarje an daura masa aure da Jessica."

22/06/2022

Ƴan Najeriya Sun Gaji Da Jam’iyyun PDP Da APC, Cewar Gwamnan Jihar Edo

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ce ‘yan Nijeriya ba su da sha’awar manyan jam’iyyun siyasar kasar nan guda biyu – PDP da APC, kawai suna neman canji ne.

Obaseki yayin da yake hira da gidan Talabijin na AIT, bayan Kammala zaben gwamnan jihar Ekiti, ya bayyana cewa makomar siyasar kasar nan tana canzawa.

Gwamnan Edo ya ce, “Ta yaya PDP a tarihin ta na girma ace ba ta yi nasara Ba? Ba ta zo na biyu ba ma.

Don haka, za ku iya ganin cewa wani abu yana faruwa. Makomar siyasarmu a kasar nan tana sauyawa.

21/06/2022

Ahmed Lawan ya fafata zaben fidda gwani na Sanatan Yobe kuma shine yayi nasara ~ shugaban APC

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address


No 25, Madatai Street
Kano
700151