Labarai24
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Labarai24, Media/News Company, Kano.
27/01/2026
Zargin badakalar Naira biliyan ɗaya: Kotu ta tsare shugaban hukumar KANSIEC da wasu mutane biyu
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC), Sani Malumfashi, tare da Sakataren hukumar, Anas Muhammed Mustapha, da Ado Garba, mataimakin darakta, bisa zargin badakalar kuɗi har Naira biliyan ɗaya.
Mai shari'a James Omotosho ya umarci a tsare su a gidan gyaran hali na Kuje, Abuja, bayan sun musanta laifuka guda shida da hukumar ICPC ta tuhume su da su.
Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga Janairu domin duba buƙatar belinsu.
ICPC ta zarge su da karɓar kuɗaɗe Naira miliyan 450, Naira miliyan 310 da Naira miliyan 260 ba bisa ƙa’ida ba, tsakanin Nuwamba da Disamba 2024, wanda aka ce na haram ne.
19/01/2026
DA DUMI-DUMI: Gwamna Abba na ganawa da Tinubu a yayin da yake shirin sauya sheƙa zuwa APC
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf a yanzu haka na ganawa da shugaban ƙasa Tinubu a fadar shugaban ƙasa dake Abuja kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Gwamnan sanye da jar hula da babbar riga ya isa fadar shugaban ƙasa da karfe 4:10 na yammacin yau.
06/08/2025
Kwamishinan da ya yi belin wanda ake zargin dilan miyagun kwayoyi ne a Kano, ya yi murabus
Kwamishinan sufuri na jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye mukaminsa bayan da aka kammala bincike kan rawar da ya taka wajen bayar da beli ga wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ta nuna cewa kwamishinan ya yi murabus ne domin kare mutuncin gwamnatin Kano da ke da akidar yaki da fataucin kwayoyi da sauran laifuka.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano
700104