A.I.A
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from A.I.A, Tutor/Teacher, Kano.
`BABBAR NI'IMAR DA ALLAH YA YI MAKA WACCE TA ISHE KA SAMUN KWANCIYAR HANKALI DA NUTSUWA`
🕋🕋🕋🕋🕋🕋🕋🕋
1️⃣- Musulunci : Babbar ni'ima ita ce Allah Ya shiryar da kai zuwa Musulunci. Yayin da wasu ke bautar gumaka, rana, duwatsu, bishiyoyi, ko kuma suke rayuwa cikin duhun bata, Allah Ya ba ka damar saninSa da bauta Masa Shi kaɗai.
Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:
﴿بَلِ اللَّهُ يَمُنُّ عَلَيْكُمْ أَنْ هَدَاكُمْ لِلْإِيمَانِ إِنْ كُنْتُمْ صَادِقِينَ﴾
"A'a, Allah ne Ya yi muku ni'ima da Ya shiryar da ku zuwa ga imani idan kun kasance masu gaskiya." (Suratul Hujurat: 17)
2️⃣- Imani : Idan ka samu cikakken imani, ka samu babban rabo na rayuwa. Imani yana kawo natsuwa, kwanciyar hankali da bege ko da a lokacin ƙunci.
Allah Ya ce:
﴿الَّذِينَ آمَنُوا وَتَطْمَئِنُّ قُلُوبُهُمْ بِذِكْرِ اللَّهِ ۗ أَلَا بِذِكْرِ اللَّهِ تَطْمَئِنُّ الْقُلُوبُ﴾
"Waɗanda s**a yi imani, zukatansu kuma suke samun natsuwa da ambaton Allah. Ku sani, da ambaton Allah ne zukata suke samun natsuwa." (Suratur Ra'ad: 28)
Duk wanda ba shi da Imani komai jin daɗinsa a Duniya a wahale ya ke
{وَمَنْ أَعْرَضَ عَن ذِكْرِي فَإِنَّ لَهُ مَعِيشَةً ضَنكًا} [طه:124].
3️⃣- Lafiya Jari : Kana gani, kana ji, kana tafiya, kana magana, kana tunani. Waɗannan ni'imomi ne masu girma da mutane da yawa ba sa lura da su sai lokacin da s**a rasa su.
Manzon Allah ﷺ ya ce:
نِعْمَتَانِ مَغْبُونٌ فِيهِمَا كَثِيرٌ مِنَ النَّاسِ، الصِّحَّةُ وَالْفَرَاغُ» رواه البخاري.
"Ni'imomi biyu ne mutane da yawa suke tafka asara a cikinsu: lafiya da lokacin hutu." (Sahihul Bukhari)
Wani yana da dukiya, mulki da matsayi, amma ba zai iya tafiya da ƙafafunsa ba, ko gani da idanunsa ba, ko magana da bakinsa ba. Saboda haka, idan kana da lafiya, ka sani kana cikin wata babbar ni'ima.
4️⃣- Tsaro da Kwanciyar Hankali Daya daga cikin manyan ni'imomin Allah shi ne ka wayi gari cikin aminci ba tare da tsoro ba.
Manzon Allah ﷺ ya ce:
«مَنْ أَصْبَحَ مِنْكُمْ آمِنًا فِي سِرْبِهِ، مُعَافًى فِي جَسَدِهِ، عِنْدَهُ قُوتُ يَوْمِهِ، فَكَأَنَّمَا حِيزَتْ
🌷 HIKIMAR KWANCIYA BACCI DA ƁARIN DAMA 🌷
ــــــــــــــــــــــــــــــــــــ
Annabi Muhammad ﷺ idan zai kwanta barci, yakan kwanta ne da ɓarin dama, kuma ya hori al’ummarsa da su yi haka. Wannan yana ɗauke da hikima mai girma ta addini da kuma ta lafiyar jiki.
Zuciyar ɗan Adam tana a ɓangaren hagu na ƙirji, ita ce cibiyar rayuwar jiki baki ɗaya. Idan mutum ya kwanta yana matsa mata, hakan na iya rage mata sauƙin gudanar da aikinta yadda ya kamata. Saboda haka, kwanciya da ɓarin dama na taimakawa zuciya ta yi aikinta cikin sauƙi wajen tura jini zuwa sassan jiki.
Haka nan, a aikin Hajji ana yin ɗawafi ne ta ɓangaren hagu, domin zuciya ta kasance tana fuskantar Ɗakin Allah — Ka’abah — cikin ikhlasi da ƙaunar Ubangiji.
🌺 اللهم يا مقلب القلوب ثبت قلبي على دينك 🌺
🌞 BARKANKU DA SAFIYA 🌞
✍️ ABDULMUMINI IBRAHIM ABDULMUMIN
مدرسة الوفاق لتحفيظ القرآن الكريم غومجا
Madrsatul wifaq li Tahfizil Qur'ani
Sabuwar Gwammaja Layin Alh Idi Bala
Hasken makaranta/ Musabaƙa
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano