Kano Observer Hausa
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Kano Observer Hausa, Media/News Company, Kano.
17/10/2021
KANO UPDATE: Jamiyyar APC ta kasa ta goyi bayan Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam'iyyar na jihar Kano.
Daraktan yada labaran jam'iyyar APC na kasa, Alhaji Salisu Na'inna Danbatta ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio Kano.
Danbatta ya ce, tsarin jamiyyar shi ne duk inda ta ke da Gwamna to shi ne jagoran jam'iyya.
Saboda haka duk inda aka yi zabe sabanin wannan to ba halastacce bane, kuma ya saba da tsarin jam'iyyar APC.
Ya kara da cewa "Gwamna ko mai babban mukami idan bamu da Gwamna a jiha shi ne gaba a jam'iyya, a duba a gani wane zabe ne aka yi shi a inda hukumar zabe ta turo wakilai?".
"Wane zabe ne jami'an tsaro s**a je s**a tabbatar da tsaro a wajen? Wannan shi ne sahihin zaben da muka sani a jihar Kano."
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan zaben shugabannin jam'iyyar APC na jihohi wanda ya bar baya da kura a wasu jihohin Najeriya.
An samu rabuwar kai a jihohin Neja, Kwara, Legas da kuma jihar Ogun da sauran su.
A nan Kano ma tsagin Gwamna Ganduje ya gudanar da zabensa tare da ayyana Alhaji Abdullahi Abbas a matsayin wanda ya yi nasarar zama shugaban jam'iyyar ta APC.
A daya bangaren shi ma tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya jagoranci nasa wanda ya ayyana Alhaji Ahmadu Haruna Danzago a matsayin sabon shugaban jamiyyar.
17/10/2021
MUHAWARA : Ra'ayin Al'ummar Jahar Kano Ya rabu kashi Biyu. Inda Tsagin Gwamna Ganduje su zabi {Abdullahi Abbas} a Bangare guda kuma tawagar Al'ummar Kano bangaren Shekarau su Zabi ( Ɗanzago ) Shin cikinsu waye Zabinku ?
20/09/2021
NFF zata karrama tsoffin 'yan wasan Super Falcons na1999
A wannan Litinin 20 ga watan Satumba Hukumar Kwallon kafar Najeriya NFF zata karrama tsoffin tawagar ‘yan matan Super Falcons ajin shekarar 1999 wadanda s**a kai wasan daf da na kusa da na karshe na gasar cin kofin duniya na mata a Amurka.
Tawagar wanda kaftin Florence Omagbemi ke jagoranta, ta doke Koriya ta Arewa da ci 2-1 a filin Rose Bowl na Pasadena, Mercy Akide da Rita Nwadike, s**a zuru kwallayen a wancan lokaci, kafin ta sha kashi a hannun Amurka da ci 7-1.
A yayin wannan kasaitacen buki a Hotel Eko dake birnin Lagos za’a karrama mambobi tawagar mata ta shekarar 1999 su goma sha biyar da kuma koci Ismaila Mabo, inda Takwas daga cikinsu s**a taso daga kasar Amurka, sai dai abin takaici, daya daga cikin ‘yan wasan tsakiya na tawagar dake yawan kai hari, Ifeanyi Chiejine ta mutu a bara.
A bukin karrama ‘yan wasan Najeriya karo na farko da ya gudana a shekarar 2018 an samu bakwancin Shugaban FIFA Gianni Infantino sannan Shugaban CAF a lokacin Ahmad Ahmad.
19/09/2021
Daga wace Karamar Hukumar kuke Kallonmu a Jihar Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Kano