Haduwar masoya
MEZAISA KUFARA GAJIYA da uzuri da kukasabayimin SO
20/09/2024
LABARIN WANI MAKAHO DA ABOKINSA
Jiya naje ziyara gidan wani Abokina wanda makaho ne. Saboda da daddare ne, sai ya yi wani abinda ya zamto mini darasi. Muna shiga cikin gidan sai ya kunna hasken gidan. Ni kuma sai nake tambayar shi: "menene yasa ka kunna haske dukda kuma baka gani?".. Sai ya fashe da dariya sosai yana shiwa, sai ya kashe wutan ya nufi kitchen, bayan mintuna kaɗan sai ya fito da butan shayi da ƙwai 🥚 a soye ya ajiye su tsaf akan tebur, sannan sai ya kunna haske.....
Abunda ya faɗa ya sanya ni ƙwalla, saboda yace dani, Mallam Yasir, Mallam Yasir! Bana kunna hasken nan saboda buƙatar kaina bane ko kuma don inada buƙatar hasken, na kunna ne saboda kai kana buƙatar hasken tunda kai ba makaho bane kamar ni"....
Sai ya tambaye ni, Mallam Yasir!!! Sau nawa ka kashe wa wassu haske saboda kai baka buƙatar hasken?"... Na tsaya nayi tunani akan wannan magana tashi sosai....
Nima anan ina tambayar ƴan'uwa na wannan tambaya a yau...
Sau nawa muka kashe wa wassu hasken muka hana wassu ganin hasken alhali suna cikin duhu?
Menene ya sa ka shaƙe asusun bankin ka da maƙudan kuɗi alhali ga Ɗan ƙanin ka ko yayan ka yana yawo babu takalma?
Menene ya sa zaka jefar da tsoffin tufafin ka alhali ga wani caan yana tafiya kusan tsirara?
Menene ya sa abinci ke ruɓewa a gidan ka alhali ga wani caaan yana kwana ya wuni da yunwa?
Menene ya sa zaka ga damammaki na business ka ɓoye ka ƙi bayyana su ga abokan ka?
Menene ya sa Ubangiji Zai kai ka wani mataki da zaka iya sakawa wani aiki ko promotion, ammana Ka ƙi yin hakan saboda shi ba dangin matar ka bane ko kuma don uwarku ba ɗaya ba?
Menene ya sa ka ke ɓatanci ga Ƴan'uwan ka don kawai baka son wassu su taimaka musu?
Ko wani tambaya dake sama daidai yake da "KASHE HASKE"
Akwai abubuwan da s**a kamata mu mayar da hankulan mu a kai a matsayin mu na ƴan Adam...
Taimakon wasu shine gaskiyar addini, taimakawa gajiyayye, da duk wani mai buƙatar hakan. Mu zamto muryar waɗanda muryoyin su basa jiyuwa.... ✍️ Daga naku
10/12/2023
10/12/2023
Mezaiyabayarwa
Asadakina
Click here to claim your Sponsored Listing.