Muryar Arewa Reporters
Muryar Arewa Reporters Shafi ne na samo labarai masu muhimmanci dake faruwa a sassan Duniya
24/01/2026
Iran ta inganta mak**ai masu linzaminta zuwa mataki na ban mamaki
tun bayan Gwabza yaƙin tsakanin Iran da Isra’ila na Tsawon kwanaki 12.
Kakakin ma’aikatar tsaron Iran ya ce ƙasar tana da mak**an roƙa masu inganci da ƙarfi fiye da waɗanda aka yi amfani da su a lokacin yakin kwanaki 12
Brigadier Janar Reza Talaei-Nik ya magantu a ranar Asabar cewa Iran ta kuma ƙara yawan mak**an roƙanta.
Gwamnatin Kano Ta Musanta Wani Rahoto
Gwamnatin Jihar Kano ta musanta wani rahoto da wata kafar yaɗa labarai ta wallafa, wanda ke zargin cewa umarnin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar na dakatar da tura takardu zuwa ofishinsa ya janyo tsaiko ko durƙushewar harkokin gudanarwa a jihar.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Umar F. Ibrahim, ya sanya wa hannu, gwamnatin ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya marar tushe, tana mai cewa ba ya da hujjar doka ko gaskiya.
Sanarwar ta bayyana cewa an bayar da umarnin ne a ƙarshen watan Disamba, bayan karewar aikin kasafin kuɗin shekarar da ta gabata, yayin da sabon kasafin ke gaban Majalisar Dokoki.
Gwamnatin ta jaddada cewa manufar umarnin ba ta tsaya kan tsaida ayyukan mulki ba, sai dai ƙarfafa da’a da tsari a harkokin kuɗi, domin hana kashe kuɗaɗe ba tare da izini ba da kuma kare jihar daga matsalolin binciken kuɗi da shari’o’i a gaba.
Ta kuma tabbatar wa al’umma cewa ayyukan gwamnati, musamman a fannonin tsaro, lafiya, ilimi da tsafta, sun ci gaba da gudana yadda ya k**ata bisa tanade-tanaden doka.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Address
Kano