Katsina Reporters

Katsina Reporters

Share

Shafin Katsina Reporters jarida ce da ke kokarin kawo maku ingantattun labarai na gaskiya ciki da wajen jihar Katsina.Call for more Inquiry TEL: 09038333537

Photos from Katsina Reporters's post 12/07/2026

Masari Ya Buƙaci Mambobin APC Su Ƙara Haɗa Kai Domin Nasarar Tinubu da 'Yan Takarar Jam'iyyar a 2027

Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Siyasa da Sauran Lamura, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, ya yi kira ga mambobin Jam'iyyar APC a Jihar Katsina da su ƙara ƙarfafa haɗin kai tare da bunƙasa ayyukan jam'iyyar domin tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran 'yan takarar APC a babban zaɓen shekarar 2027.

Masari ya bayyana hakan ne yayin wani taron dabarun siyasa da ya gudanar da shugabanni da mambobin ƙungiyar Wazirin Tinubu Ambassador Movement a Katsina. Ya ce nasarar APC na ta'allaka ne kan haɗin kai, jajircewa da aminci tsakanin mambobinta, yana mai ƙarfafa su da su ci gaba da kusantar al'umma, su ƙarfafa tushen jam'iyyar daga matakin ƙasa, tare da gujewa duk wani abu da ka iya haifar da rarrabuwar kai.

Haka kuma Ibarahim Masari Ya ja hankalinsu kan jaddada ci gaba da hadin kai a jam'iyya yana buƙatar haɗin kai, mutunta juna da fifita muradun jama'a da na jam'iyyar.

A nasa jawabin, Ministan Gidaje da Raya Birane, Arc. Muttaka Rabe Darma, ya yaba da ayyukan ƙungiyar tare da ƙarfafa mambobinta su ci gaba da aiki cikin haɗin kai da bin ƙa'idojin shugabanci nagari. Shi ma Darakta Janar na ƙungiyar, Hon. Aliyu Mansur Majidadi, ya tabbatar da aniyar faɗaɗa ayyukan ƙungiyar zuwa dukkan ƙananan hukumomi 34 na Jihar Katsina domin ƙara ƙarfafa APC.

Taron ya kuma samu halartar mambobin Kwamitin Amintattu, shugabannin jiha da na ƙananan hukumomi, wakilan gundumomi da sauran jagororin jam'iyyar, inda s**a sake jaddada goyon bayansu ga Ajandar Renewed Hope da kuma shirin siyasar Tinubu/Dikko 2027.

— Katsina Reporters.

Want your business to be the top-listed Media Company in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address


No. 12, Ramadan Plaza Ƙwaɗo Ring Road Katsina
Katsina