Combat Computer Technology
Computer training, business center and consultancy services
IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA (11)
**********
Da Sunan Allah Rayayyen Sarkin da gyangyadi bai ta'ba riskarsa ba, b***e barci. Salati da aminci su tabbata bisa Ma'abocin Farkon Zance aranar da dukiya da 'ya'ya basu amfani, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa Gwargwadon girmansa.
Hakika lamarin Alqiyamah da girma yake.. Babu mai tsallake firgicinta sai wadanda Allah ya za'ba daga cikin bayinsa.
Yayin da Mala'ika Israfeelu yayi busar farko acikin Qaho, dukkan mutane basu firgita su dimauce da eehu tamkar mashayan dake tambele. Kuma wannan firgitar da tashin hankalin da sumewar bata kebanci 'yan Adam kadai ba. Domin kuwa Allah cewa yayi :
"RANAR DA ZA'AYI BUSA ACIKIN QAHO SAI DUKKAN WADANDA KE CIKIN SAMMAI DA WADANDA KE CIKIN QASSAI SU FIRGICE, SAI DAI WADANDA ALLAH YASO... "
Wato wannan firgitar zata shafi kowa da kowa. Daga nan sai kuma mutuwa ta riskesu baki daya.
Ibnu Hajr Al Asqalaniy (rah) yace "Busa ne guda biyu - ta farkon acikinta ne duk masu mutuwa zasu mutu. Wadanda Allah ya kebancesu kuma zasu suma. Idan anyi busar Qaho ta biyu kuma acikinta ne kowanne matacce zai tashi, Kuma kowanne sumamme zai farfado".
Ubangiji ya buga misali da Jarirai har sau uku game da girman tashin hankalin Alqiyamah. Ya siffata mana ita k**ar haka :
- Ranar da zaku ganta, Kowacce mai shayarwa zata jefar da abinda take shayarwa.
- Ranar da Mai ciki zata haife abinda take dauke dashi.
- Ranar dake sanya jarirai yin furfura.
Duk wanda yake so yaga yadda Alqiyamah zata kasance k**ar akan idonsa, to ya karanta surorin nan guda uku :
- Idhash Shamsu kuwwirat. (Suratut Takweer).
- Idhas Sama'un Fatarat (Suratul Infitaar).
- Idhas Sama'un Shaqqat (Suratul Inshiqaq).
Abubuwan dake gabanmu yanzu anan duniya sune k**ar haka :
- Sararin samaniya.
- Qasa.
- Duwatsu.
- Tekuna.
- Dabbobi.
- Rana, Wata da Turari.
To dukkan wadannan abubuwan Allah ya bamu labarin yadda makomarsu zata kasance aranar Alqiyamah.
SAMMAI : Allah yace "Idan sama aka kyeceta".
QASSAI : "Idan aka girgiza Qasa mutukar girgizawarta, Kuma Qasa ta fitar da nauye-nauyenta".
DUWATSU : "Ranar da za'a nike Qasa da duwatsu".
"Kuma duwatsu zasu zamanto tamkar gashin buzun da aka jeme".
TEKU : Allah yace "Kuma idan tekuna s**a kyakkece (S**a hade da junansu).
"Idan tekuna aka cinna wuta garesu".
Wato zasu hade da junansu kuma daga karshe Ubangiji zai sa su k**a da wuta baki dayansu.. (SUBHANALLAH).
DABBOBI : "Idan dabbobi aka tashesu (Domin yin hisabi atsakaninsu)
RANA DA TAURARI : "Idan rana aka tafiyar da haskenta, Idan Taurari aka gurbacesu (wato launinsu ya chanza, s**a gauraye da junansu).
Ibnu Abi Hatam ya ruwaito hadisi ta hanyar Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (ra) yana cewa "Rana da Wata da Taurari Allah zai dulmiyar dasu acikin Teku ne aranar Alqiyamah sannan ya aiko da wata iska mai Qarfi wacce zata cinna musu wuta".
Wannan kenan daga abubuwan da duk wani mai rai awannan lokacin sai ya gani da idonsa idan lokaci yayi.
Ya Allah kasa mu cika da imani ameen.
06/03/2022
GOOOD BYE L.G.A
Cikin ikon Allah yau Lahadi 6/3/2022 mun kammala program dinmu na computer training a cikin karamar hukumar Kurfi wanda ma'aikata, matasa da dalibai s**a amfana da wannan karatu da akayi.
Muma godiya ga Allah daya bamu rai, lafiya da lokacin da muka dauka domin bada wannan gudunmuwa ta ilmantar da al'umma wannan ilimi.
Godiya ta musamman ga abokan aiki Muhammad Nafi'u Yahaya da Nazifi Isah Garia tare da Financial secretary na wannan group wato Bishir Suleiman Kurfi, Kurfi local government coordinator Sani Umar da takwaranshi na Dutsinma Ibrahem Shehu Abu Hajarah, NUT chairman da dukkan wadanda s**a bada gudunmuwa ta shawarwari, lokaci da sauransu don ganin an samu nasarar tafiyar da wannan program.
Muna rokon Allah yasa wannan karatun ya zama mai albatka da alheri garesu da al'umma baki daya.
01/03/2022
DAY 1
MAI'ADUA LOCAL GOVT.
Yau 1/3/2022 cikin ikon Allah gamu a garin Mai'adua a rana ta farko domin fara computer literacy training wadanda ma'aikata, dalibai da matasa zasu amfana da wannan shirin.
Wannan program na tafiya karkashin jagorancin training manager Mal. Nafiu, local government coordinator Mal. Zakari tare da mataimakinsa Mal. Zaruku Ahmad da kuma kulawar NUT Chairman Mal. Salmanu Abba.
25/02/2022
KURFI
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Katsina