READ RIGHT EDUCATIONAL RESOURCES

READ RIGHT EDUCATIONAL RESOURCES

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from READ RIGHT EDUCATIONAL RESOURCES, Education, No. 278 Sarki Mukhtar Way, adjacent Lugga's Mosque Kofar Marusa Low-Cost Katsina, Katsina.

14/09/2024

Santi wani yanayi ne da ɗan adam ke shiga tsakanin fai da ɓoye, wanda yake samun damar tsinkayar abubuwa da dama wanda a salin-alin ba zai tsinkayesu cikin sauƙi ba.

Wani nau'in tunani ne da lokutta masu yawa dashi ne Turawa ke amfani su hasko wani abu don ciyar da al'ummar su gaba, shine abincin da Mawaƙa ko Marubuta ke ciyar da ruhinsu dashi, wanda daidai ƙoshinsa (ruhin), daidai tunbatsar da zai yi tare da zaiyana irin basira ko fasahar dake danƙare cikin ƙirjinsu.

Yayin da ake buƙatar yin nazari mai kyau don samar da wani abu ko mafita kan wani lamari, musamman Turawa, s**an haɗa kan masana su kaisu wani wuri na ɗebe kewa, mai ƙarancin hayaniya, a basu kulawa ta musamman wanda ya ƙunshi abin ci da abin sha domin samun damar tsinkayar abinda zai amfani al'umma, sau tari ma sai suna tsakiyar cin abinci suke fara tattauna mas'alar, wannan ya kawo hasashensa wancan ya kawo tsinkayensa har dai a cimma mawafaƙa.

Kamar haka ne Marubuta ko Mawaƙa ayayin da suke buƙatar samar da wani kari na musamman ko ƙirƙiro wani labari mai ban ƙaye, s**an yi amfani da irin wannan damar ne domin dafa tudun mun tsira, wanda s**a haɗa da wurare masu ban sha'awa da nishadi, lokacin cin abinci, yayin da suke tsuguno/bahaya, yayin barci, yayin nishadi, yayin kaɗaici, wasu ma suna samun kari ko kanun labaran su a yayin da suke wanka (shiyasa duk lokacin da ka watsa ruwa a gadon bayanka ya ratsaka sosai, zaka ji wani tunani mai haɗe da ilhama na ratsaka, kar ka sake ya tafi hakanan baka ribaceshi ba).

Irin wannan abin shi ake kira da Santi, amma mu a Hausance ko a Arewance sai muka alaƙanta Santi da wani abin yin ba'a, tsokana ko raha a tsakaninmu a duk lokacin da mutum yayi shi, wanda hakan yasa kowa yake ƙoƙarin nisanta kansa dashi, maimakon muyi amfani dashi don goge matsokacin tunaninmu tare da gurje dattin da yayi wa cigabanmu tarnaƙi ta hanyar tunani mai kyau wanda yake ƙyastuwa a rai daga galudayar Santi.

Kayi tsan da ranka, zaka ga cewa a duk lokacin da kake kai kaɗai, ko kake cin wani abu mai daɗi ko wanda ka daɗe baku haɗu ba (mafiya lokutta mun fi alaƙanta rake da santi), ko kake cikin nishaɗi zaka ga cewa a waɗannan lokuttan tunani mai ƙyau yafi ƙyastuwa ko ziyartar ranka, duk wani abu daka kasa warware shi tsawon lokaci a ɗan wannan lokacin sai kaga ka lalubo bakin zaren cikin sauƙi.

Mutane na rasa wannan damar ta hanyar cewa haba santi ne, ba wani abu ne mai muhimmanci ba, ko gudun kar a musu dariya ko tsokanar su, sai su bari har wannan damar ta suɓuce, don kauce wa dukan biyun abinda ya kamata sai ka samu takarda da biro, kai ko a wayarka ne ka rubuta shi, domin irin wannan tunanin madamar ya zurare ba lallai ka kuma jinsa a ranka ba. Ta haka sai kaga ka kuɓuta daga zargin mutane kuma ka amfana daga taskar Santi.

Mustapha Muhammad Gimba,
14th September, 2024.

22/12/2021

In Progress!!!

15/11/2021

Our CEO at work!

Cc: Aliyu Nasir Kankara

Want your school to be the top-listed School/college in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


No. 278 Sarki Mukhtar Way, Adjacent Lugga's Mosque Kofar Marusa Low-Cost Katsina
Katsina

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00
Saturday 09:00 - 17:00
Sunday 09:00 - 17:00