AID Multimedia Hausa

AID Multimedia Hausa

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from AID Multimedia Hausa, Media/News Company, Lagos.

Photos from AID Multimedia Hausa's post 05/06/2026

A Na Daf Da Kafa ’Yan Sandan Jihohi A Najeriya, in ji Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba a tattaunawar kafa rundunar ’yan sandan jihohi, inda ake sa ran gabatar da gyaran kundin tsarin mulki nan ba da jimawa ba domin ba da damar aiwatar da shirin.

Babban Ma’aikacin Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da aka yi a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja ranar Alhamis, wadda ta haɗa manyan jami’an gwamnati da shugabannin majalisun dokoki kan batun kafa ’yan sandan jihohi.

Gbajabiamila ya ce an fara nazari da tattaunawa kan yadda za a kafa rundunar tun watanni uku zuwa huɗu da s**a gabata bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuma an samu ci gaba mai yawa a aikin.

Ya bayyana cewa kafa ’yan sandan jihohi ba abu ne da za a yi cikin gaggawa ba, domin akwai batutuwan kundin tsarin mulki da dokoki da dole ne a tantance su sosai kafin aiwatarwa.

A cewarsa, yanzu hankalin masu ruwa da tsaki ya karkata ne kan yadda za a yi gyaran kundin tsarin mulki, sannan daga baya a samar da dokokin da za su ba da cikakken iko da tsarin gudanar da rundunar.

Ya ƙara da cewa mafi yawan ’yan Najeriya da masu ruwa da tsaki sun amince da bukatar kafa ’yan sandan jihohi, inda muhawarar yanzu ba ta kan ko a kafa su ko a’a ba, sai dai yadda za a samar da ingantaccen tsarin doka da gudanarwa domin su yi aiki yadda ya k**ata.

Gbajabiamila ya ce za a gabatar wa Shugaba Tinubu cikakken rahoto kan sak**akon ganawar domin ci gaba da matakan da s**a dace.

A cewarsa, manufar kafa ’yan sandan jihohi ita ce ƙarfafa tsaron cikin gida, inganta tattara bayanan sirri daga matakin ƙasa da kuma bai wa gwamnatocin jihohi damar magance matsalolin tsaro cikin sauri da inganci.

Shugaba Tinubu ya sha bayyana cewa tsarin ’yan sandan jihohi na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen fuskantar ƙalubalen tsaro da ke addabar ƙasar nan, tare da ƙara kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ganawar ta samu halartar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin; Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu; Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi; da Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Tunji Disu, tare da sauran manyan jami’an gwamnati.

03/06/2026

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar da Shalkwatar Hukumar 'Great Green Wall' Zuwa Kano Don Inganta Aiki

Gwamnatin Tarayya ta ɗauki gabarar daidaita ayyukan hukumar yaƙi da kwararar hamada ta kasa, wato National Agency for the Great Green Wall (NAGGW), inda ta mayar da babban ofishinta na gudanar da ayyuka daga birnin tarayya Abuja zuwa jihar Kano.

Ministan Muhalli, Balarabe Abbas Lawal, ne ya bayyana hakan, inda ya bayyana cewa matakin na kunshe ne a karkashin tsarin 'Renewed Hope Agenda’ na Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Manufar hakan ita ce tallafa wa hukumar don ta gudanar da ayyukanta cikin hanzari da nagarta a jihohin da abin ya shafa.

Shirin na 'Great Green Wall' babban yunkuri ne na Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) da ya kunshi kasashe 11, da nufin yaki da kwararar hamada, lalacewar kasa, da kuma radadin sauyin yanayi a yankin Sahel da Sahara.

A nan Najeriya, shirin ya karkata ne a kan jihohi 11 na gaba-gaba da hamada ke barazana musamman ga rayuwarsu, wadanda s**a hada da: Bauchi, Borno, Gombe, Jigawa, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto, Yobe, Zamfara, da kuma Adamawa.

Ministan ya kara da cewa, babban burin hukumar shi ne shimfida dangar bishiyoyi (Green Wall) mai nisan kilomita 15 a fadi, da kuma tsawon kilomita 1,500 domin kare muhalli, rage radadin sauyin yanayi, samar da wadatar abinci, da kuma rage radadin talauci a karkara.

Tun lokacin da aka kaddamar da shirin a shekarar 2013, kafin daga bisani a mayar da shi cikakkiyar hukuma a 2015, an samu manyan nasarori k**ar haka:

Kafa dangar kariya daga iska da yashi (shelterbelts) fiye da guda 100.

Gina madatsun ruwa na sola da iskar gas guda 159 don samar da ruwan sha.

Daukar matasa guda 600 a matsayin dogaran daji (forest guards).

Samar da gonakin bishiyoyin itatuwa na (orchards and woodlots) guda 240 don bunkasa kudin shiga.

Malam Balarabe Abbas Lawal ya jaddada cewa, wannan sauyi zai magance kalubalen da hukumar ta dade tana fuskanta na gudanar da ayyuka daga ofishin haya a Abuja, wanda ke nesa da ainihin inda ayyukan suke a Arewa. Komawa Kano, wadda ita ce cibiyar yankunan da ayyukan s**a shafa, zai ba da damar sanya ido, da samar da kyakkyawar alaka tsakanin gwamnatocin jihohi, sarakunan gargajiya, da al'ummomin yankunansu.

Jihar Kano riga ta saba da irin wadannan ayyuka, domin tana dauke da ofishin tsara shirye-shiryen dashen bishiyoyi (APCU) tun a shekarar 1988, wanda yanzu ba a amfani da shi yadda ya k**ata tun bayan kammala shirin Bankin Duniya na dashen bishiyoyi a yankunan fari (Arid Zone Afforestation Programme) a shekarar 1996. Wannan cigaba a yanzu zai cigaba a hukumar ta NAGGW.

Daga karshe, Ministan ya bayyana yakinin cewa wannan mataki na kusanto da hukumomi kusa da inda suke aiki zai kawo sauyi na gaske ga rayuwar miliyoyin 'yan Najeriya da ke zaune a yankunan da kwararar hamada ke addaba.

Want your business to be the top-listed Media Company in Lagos?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address


Lagos