Taskar Labari

Taskar Labari

Share

We sell,promote and advertise any type of beauty product. We welcome beauty training sponsors and be

30/01/2023

HANA WANI HANA KAI!
MBC WRITERS
Jigo: Siyasa ba da gaba ba.

"A yammacin yau kuma an tashi da wani mummunan labari na mutuwar 'yar takarar sanata Hajiya Nafisa Ɗangaske..."
"Innalillahi!" Hajiya Saude ta faɗi, tare da dafe ƙirjinta cikin tashin hankali da ba a sanya masa rana. Jikinta na rawa ta matso gaban talabijin ɗin don tabbatar da ba kunnenta ne ke yaudarar ta ba, aiko gani ya kori ji, domin har bidiyon gawar an hasko cikin jini kamar an yanka rago, ana mai ƙara bayyana hatsarin mota ne ya ritsa da ita.
Da gudu Hajiya Saude ta shiga sashen mijinta wato Sanata Ali Ɗangaske, sai dai bayan ta bayyana a gabansa ta kasa cewa uffan domin ba ta san da kalmomin da za ta iya sanar da shi ƙanwarsa uwa ɗaya uba ɗaya ta rasu ba.
Sanata ya ce, "Lafiya? Me ya faru na ga kina rawar jiki kamar 'yar mazari."
"Yar uwarka...'Yar..." Ya..." Maganar ta maƙale a maƙoshinta.
"Me ya faru da ita?" Ya tambaya cikin nutsuwa.
"Ta rasu..." Ta ƙarasa da azababben kuka, tare da runtse ido don ba za ta iya ido biyu ko ganin halin da maigidan nata zai shiga ba.
Jim kaɗan ba tare da ta ji motsinsa ba yasa ta yi saurin buɗe ido, a tunaninta ya yanki jiki ya faɗi ko wani abu makamancin hakan, sai dai bisa al'ajabi ta ga wani murmushi mai bayyana tsantsar farin ciki a kan fuskarsa.
'Shin zaucewa ya yi?'
Sanata Ali Dagaske ya saki wani murmushin da ya ƙara bayyana fararen haƙoransa, "Ban zauce ba, lafiya sumul nake!"
A wannan lokacin Hajiya Saude ta fahimci zancen zuciyarta ya fito fili.
Sanata Ali Ɗangaske ya ci gaba da cewa, "Ai tun daga shigowarki na san abin da ya kawo ki, domin na san dama yau za ta mutu!"
Hajiya Saude ta zaro ido kamar za su bulloƙo don tsabar tsorata, muryar ta na rawa ta ce, "Me kake nufi?"
Maimakon ya amsa, sai ya bushe da dariya kamar ba zai daina ba, daga bisani kuma ya murtuƙe fuska tamkar ba shi yake dariyar ba.
"Duk wanda ya shigo hanyata a siyasa ko waye shi sai na kawar da shi, domin duk abokin karawata abokin gaba na ɗauke shi, har da ita ƙanwar tawa! Tun da bata ji bari ba yanzu ta ji faufau."
Yana gama faɗin hakan ya kaɗa rigarsa ya shige ciki, ya bar amaryar tasa cikin al'ajabi. Tabbas lamarin mijinta da uwar gidansa abin tsoro ne, yanzu ta yarda a kan siyasa zai iya aikata komai.
Bata taɓa tunanin takun saƙar sa da 'yar uwarsa zai kai haka ba.
A baya ta yi tunanin shawarwarinta gare shi za su yi amfani ashe dai shuka dusa take.

***

Alhaji Ali da Ƙanwarsa Nafisa su kaɗai Allah ya bai wa iyayensu.
A zaɓen da ya gabata, Alhaji Ali ya yi nasarar samun kujerar sanata, wacce ƙanwarsa Nafisa tana ɗaya daga cikin hatiman nasararsa duba da irin fafutukar da ta yi wajen yaƙin zaɓensa. Kasancewar ta sananniya cikin al'umma hakan yasa ta yi saurin karkato akalar al'umma zuwa ga zaɓen ɗan uwan nata.
Sai dai bayan lashe zaɓen tuni ya mance duk wannan rawar gani da Hajiya Nafisa ta yi, alkawaruka da ya mata da 'yan allazi-wahidin dake bibiyarta kamar raƙumi da akala duk ya ƙi cikawa. Ta bibiye shi, ta bibiye shi amma ya yi kunnen uwar shegu da buƙatunta.
Yau da gobe asarar mai rai, zaɓe ya zagayo. Kwatsam Alhaji Ali ya ji labari ƙanwarsa ta fito neman takarar kujerar sanata.
A fusace ya je har gida ya same ta, "Ke? Yanzu don tsabar wulakanci har wuyanki ya kai yankar da zaki fito takarar zaɓe da ni?"
Hajiya Nafisa ta yi murmushi, sannan ta ce, "To mene ne a ciki tun da dokar ƙasa ta sahale min? Ai kawai kowa tashi ta fishe shi!"
"Sam ba zan laminci faɗuwa ba! Don haka ki yi saurin janye wannan banzan ƙudirin naki, don ni duk abokin takara ta maƙiyi ne da zan iya aikata komai wajen take sa na wuce, kuma kasancewar ki ƙanwata ba zai canza komai ba!"
Hajiya Nafisa ta yi shewa, "Ahayye! Ai duk wadda ya ce a yi wasan jifa to ya taka dutse ne, ni ma murucin kan dutse ce ban fito ba sai da na shirya don haka mu zuba ga fili ga mai doki!"
"Saura sukuwa!" Ya fice cikin fushi.

'Yan uwa da abokan arziki sun shawarce su tun da neman takara allura ce cikin ruwa mai rabo ka ɗauka, su yi siyasa ta fahimtar juna ba tare da ƙullatar juna ba. Kowa ya yi fafitikar neman nasararsa ba tare da yin wata gaba ba. Duk wadda ya rasa kar ya riƙi wanda ya yi nasara a zuci ko wani abu makamancin haka, sai dai duk su biyun kowa neman mulkin yake ido rufe, don haka kowa ya ɗaura ɗambar kai ɗan uwansa ƙasa ta kowanne hali.
Hajiya Nafisa ta shiga kitsa sharri da tuggu kala-kala wajen ganin ta baƙanta ɗan uwan nata, duk lokacin da fito kamfen sai ta masa wankin babban bargo wajen bayyana wa al'umma gazawarsa da laifukansa na baya har ma wanda bai aikata ba.
Ganin hakan yasa ta fara jan ra'ayin wasu mutanen da suke ganin za ta yi adalci tun da har za ta iya fita gaban al'umma ta faɗi aibun rabin jikinta, ganin wannan nasara ya sa ta ƙaro himma wajen ganin ta take ɗan uwan nata da tukubar makirci.
Shi ma a sashensa bai gaza ba, domin ko 'yan takarar da su kai zaɓen fidda gwani a jam'iya ɗaya bai musu sauƙi ba b***e wannan dake jam'iyyar adawa kuma babbar barazana gare shi.
Wannan adawa ta su ta yi tsamarin da ta fi ƙarfin a kwatanta don har tura wa juna 'yan bangar siyasa suke, wadda duk ranar da aka yi toho-mu-gama tsakanin 'yan bangar munin abin ba ya iya kwatantuwa.
Siyasa na ƙara matsowa, ganin Alhaji Ali yana faman rasa kujerarsa ta sanata sai ya koma ga bokaye da malamai wajen ganin an masa duk abin da za a yi masa don kawo karshen takarar 'yar uwarsa, inda wani boka ya masa alƙawarin ana saura sati ɗaya da fara zaɓe komai zai zo ƙarshe.
Haka Alhaji Ali ya yi zaman dirshan yana jira, don haka jin wannan labarin na mutuwar 'yar uwar tasa ya sa ya ji a ransa aiki ya yi, ba tare da ya yi tunanin ko Allah ne ya aiko ba.

***
Bayan an yi zaɓe, jira Alhaji Ali yake kawai ya maimaita kujerarsa kwatsam! Aka sanar da cewa bai yi nasara ba.
"What! Wallahi hakan ba zai taɓa yi yuwa ba, ta yaya ɗan takarar da ban ma ɗauke shi a komai ba zai yi nasara a kaina? Ba zai saɓu ba bindiga cikin ruwa, daga nan har kotun ƙoli sai na je akan kujerata. Akan me!"
Matarsa Saude ta yi murmushin takaici ta ce, "Dama ɗan hakkin da ka raina shi ke tsone maka ido. Sa'in da nake faɗa muku gaskiya toshe kunnenku kuka yi, a wannan lokacin da idonku ya makance ku ka sa kan ku gaba wajen zayyano aibu da ƙullatar juna kai da ƙanwarka a wannan lokacin shi kuma ya zage wajen bayyana wa al'umma manufarsa kuma s**a gamsu.
Wataƙil ko da Hajiya Nafisar ma na raye haka zaku yi faɗuwar guzuma saboda hana wani hana kai ne. Amma yanzu zaka gane da kyakkyawar manufa ake cin nasarar zaɓe ba siyasa da gaba ko hamayya ba."

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Potiskum?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Potiskum