Albani Grassroot Mobilization AGM

Albani Grassroot Mobilization AGM

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Albani Grassroot Mobilization AGM, Political organisation, Samaru.

Photos from Albani Grassroot Mobilization AGM's post 15/10/2024

HONOURABLE ADAMU ADAMU MATAZU (JAGORAN GAMAYYAR ƘUNGIYOYIN MATASAN AREWACIN NAJERIYA) YA ZIYARCI DAN TAKARAR SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR SABON GARI HON. SHEIKH JAMILU ABUBAKAR ALBANI TARE DA TAWAGAR SA KUMA SUN TABBATAR DA GOYON BAYAN SU A GARE SHI.

A daren Lahadin ta gabata Shugaban gamayyar ƙungiyoyin matasan Arewacin Najeriya, kuma haifaffen garin Samarun Sabon Garin, Zaria Hon. Adamu Adamu Matazu ya ziyarci dan takarar shugaban karamar hukumar Sabon Gari Hon. Sheikh Jamilu Abubakar Albani tare da tawagar sa domin mara masa baya bisa takarar shugaban karamar hukumar Sabon Gari da yake yi.

Hon. Adamu Adamu Matazu a bayanin sa ya bayyana cewa ya kawo wannan ziyara ne tare da jama'arsa domin su nuna goyon baya ga Hon. Sheikh Jamilu Abubakar Albani a bisa wannan takarar da yake yi na Shugaban karamar hukumar Sabon Gari. Ya kara da cewa sun duba sunga a kaf cikin yan takarkarin ba wanda yafi shi cancanta, kuma a damammakin da ya samu a baya na shugabanci yayi iya bakin kokarin sa gurin taimakon jama'a da ciyar da yankin mu gaba. Saboda haka ne ya ga ya dace a mara masa baya domin samun cigaban al'ummar mu da yankin mu baki daya.

Daga bisani, Hon. Sheikh Jamilu Abubakar Albani yayi godiya kuma ya nuna farin cikinsa ga wannan goyon baya tare da tabbatar da cewa In Sha Allah idan Allah ya bada wannan dama zasu yi duk iya abinda zasu iya don ciyar da wannan yanki namu gaba.

Taron ya samu halartar dimbin matasa daga sassa daban-daban, da Shuwagabannin addini da masu sarauta da sauran su.

Muna Addu'a Allah ya bama Hon. Sheikh Jamilu Abubakar Albani Naasara a wannan zaɓe da muke fuskanta ya kuma musu jagora.
Ameen.

Umar Ahmad Abu Mus'ab
SABON_GARI_FIRST

23/09/2023

HONOURABLE SHEIKH JAMILU ABUBAKAR ALBANI 100 DAYS IN OFFICE, DAYS WORTHY OF CELEBRATION AND MOTIVATION.

Within 100 days in office Hon. Sheikh Jamilu Abubakar Albani Member representing the good people of Basawa Constituency (Deputy Chief Whip Kaduna State House of Assembly and Chairman Committee on Interfaith and Religious Affairs) was able to shows his capacity by providing positive impact to his constituents in the areas of education, Empowerment and more.

In his 100 days in office Hon. Sheikh Jamilu Abubakar Albani Samaru Zaria was able to support less privilege students with scholarship within his constituency, Empowered many petty traders, Distributed Fertilizer to Farmers, Payed school fees for students of Islamic Schools, Payed Medical bills of some less privileges among many other important activities and services.

From what we saw in the first 100 days we are optimistic that many good things are coming for the benefit of the Constituents.

We pray that Almighty Allah will continue to guide him and encourage him towards his duties to provide and bring more benefits to the people he is representing.

Umar Ahmad Abu Mus'ab
Concern Constituent.

Photos from Albani Grassroot Mobilization AGM's post 25/09/2022

*SHUGABANCIN ƘUNGIYAR ALBANI GRASSROOT MOBILIZATION (AGM) TAKAI ZIYARAR GIRMAMAWA TA MUSAMMAN GA HON. MUSTAPHA SHEIKH ABDALLAH.*

A daren jiya Asabar 24 ga watan September jagorancin ƙungiyar Albani Grassroot Mobilization (AGM) ƙarƙashin jagorancin Hon.Hamisu Jaraman Samaru (Wanda Hon. Mustapha Milgoma ya wakilta) da sauran jagororin ƙungiyar sun kaima Hon. Mustapha Sheikh Abdallah ziyarar girmamawa a garin samaru.

Shugaban ƙungiyar wanda Hon. Mustapha Milgoma ke wakilta tare da mataimakin magatakardar ƙungiyar Hon. Hussaini Muhammad Gamawa sunyi cikakken bayani na abinda ƙungiyar ta ƙunsa tare da ayyukan da ƙungiyar keda kudirin aiwatar wa. Bayan haka shuwagabannin kungiyar sun nemi gudunmawa tare da goyon baya akan ƙudurorin wannan ƙungiya mai Albarka.

Daga bisani Hon. Mustapha Sheikh Abdallah ya nuna farin cikinsa da jin dadi na Ziyarar da aka kawo masa, tare da jinjina ga irin tsare-tsare masu kyau da wannan ƙungiya take dashi kuma ya tabbatar da bada gudunmawar sa a duk lokacin da aka buƙace sa. Bayan haka ya bada shawarwari musu mahimmanci domin samun nasarar dan takarar mu Sheikh Jamilu Abubakar Albani da sauran yan takarkarin Jam'iyyar APC daga sama har kasa.

Taron ya samu halartar Shugabannin kungiyar AGM daga dukkan gundumomi guda huɗu na Basawa Constituency.

Allah ya bamu Nasara ameen.

*Directorate of Media and Publicity,*
*Albani Grassroot Mobilization (AGM)*
*25th September,2022.*

01/08/2022
Want your organization to be the top-listed Government Service in Samaru?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address


Samaru