APWON Channel
Anbude wannan qungiya 30 December 2020
Qarqashin shugabancin Fadl Sabiu kura qungiyace ta gwaraza Quran
Usman Lawal Na Allah Zurmi From Zamfara State
National Musabaqah at Kwara State
Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!
Cikin Murna da Farin ciki Muna taya Malamin mu Shaikh Hafiz Dr. Goni Dahir Goni Idris Annayim Murnar Kammala Digiri Na Uku (PhD) A Fannin Qira'at Da Ulumul-Quran, A Faculty of Qur'an Na Jami'ar International University of Africa (IUA) - Sudan, Tare da samun daraja Qololuwa (Excellent).
Muna Fatan Allah Ya Kara Wa Rayuwarshi Albarka, Ya Kuma Kara Karfafa Shi A Kokarin Da Yakeyi Na Amfanar Da Al-ummar Musulmi Da ilimin Sa. Ameen.
We extend our warmest congratulations to Sheikh Dr. Goni Dahir Goni Idris Annayim on successfully completing his PhD in Quranic Intonations and its Sciences with an 'Excellent' grade from the Faculty of Qur'an, International University of Africa (IUA), Sudan.
May Allah bless his life and the Certificate Acquired Jazahullah khair
Assalaam Alaikum
04/02/2025
ALHAMDULILLAH
A Madadin Qungiyan Yan Musabaqa Na Nigeria Muna taya dan uwanmu Malaminmu Hafiz Ibrahim Siraj Adhama (Kano State) Samun qarin girma da Nasaran zama Associate Professor na "Mass Communication" bisa Qaddarawan Allah da Falalarsa,
Lalle Wannan Nasara ce babba a Rayuwa, Sannan kuma ya cancanci hakan Saboda Qwazonsa da qoqarin Inganta Ayyukansa Na Koyarwa da Ilimi, babu shakka Nasara tana zuwa ne bayan Ansha Wahala
Allah Ya Qara masa Nasara Allah yasa yan bayansa suyi koyi da Hakan.
Yusuf Muhammad Dukku
National Secretary
APWON
Alhamdulillah
An zabi Goni Dahir Goni Idris daga Nigeria acikin Alqalan Musabaqa na Duniya na 2025 a Qasar Algeria Karo na 20 muna masa fatan Alheri Allah ya bada Nasara
05/01/2025
Assalamu alaikum Warahmatullah
بارك الله لهما وبارك عليهما وجمع بينهما في خير
A madadin Shugaba Na Yan Musabaqan Nigeria Goni Aliyu Muhd Bakura muna taya dan uwanmu Hafiz Albashir Goni Usman (Borno State) Murna da Fatan Alheri bisa Niima na aure da yayi wanda aka daura jiya a Suleja,
Muna masa fatan Allah ya sanya albarka acikin auren nashi Allah ya basu zaman lafiya da zurriya dayyibah
Sanarwa Yusuf M Dukku
Secretary Apwon Nigeria
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the place of worship
Telephone
Website
Address
UDUSCIS
Sokoto