Sahaba TV

Sahaba TV

Share

Kasance da https://www.youtube.com/@Sahaba_TV domin samun Karatuttukan Malaman Sunnah a saukake.

23/07/2026

Ruko da Sunna: Mu na cikin zamanin fitina musamman a cikin addini , idan mutum bai dage da gaske ba musamman ta hanyar addu'a da kusantar maluman sunna ba; nan da nan wakilan a*r*na za su jefa masa kokwanto a cikin addinin sa.

Dan uwa ka rike zuwa karatu da bibiyar maluman sunna sannan da addu'ar dacewa, wakilan shaidan sun yawaita masu kokarin a lallai sai sun rushe Sunna , a lallai sai sun raba mutane da Hadisan Annabi صلى الله عليه وسلم .

Kura tana cin akuyar da ta wa re daga cikin 'yan uwanta ne; ma'ana duk sanda ka rabu da koyarwar sunna ba bu ruwanka da karatu da majalisan ilmi tabbas lokaci daya wadannan wakilan shaidan din za su yi awon gaba da kai; ba kayi aune ba sai ka ji ka cikin masu sukar Hadisan Annabi صلى الله عليه وسلم .

Ka lizimci maluman sunnah
Ka lizimci addu'ah.

اللهم يا مقلب القلوب ثبت قلوبنا على طاعتك .

✍🏽Abdussalam Abdullah.

9-Safar-1448H
23-7-2026.

17/07/2026
08/07/2026

Kwanannan Shek Abubakar Pharmacy Gombe ya rasu amma sam-sam ba muji 'yan uwansa sun nemi a goge bidiyon sa ba , ko za a goge shafin sa ba (Page) Na soshiyal midiya ba. Saboda ayyukan alkhayri ne makil a ciki ba bu bukatar a goge.

Amma mu duba dayan bangaren wato masu yada badala da alfasha a cikin al'umma a soshiyal midiya da zarar sun mutu sai kaji a na rokon jama'a su goge bidiyoyin su ko ka ga ana za a goge account din su, saboda sam-sam ba su yada alkhayri ba sai sharri!

Dan uwa ni da kai da kuma ke mu yi wa kanmu tambaya shin mai muke yadawa a social media ? Alkhayri muke yadawa ko sharri? Idan alkhayri ne shin mu na yi da ikhlasi (Saboda ALLAH)?
Ko don a ya be mu muke yi ? Idan sharri ne mu tuba mu daina kafin mutuwa ta riske mu a zo ana za a goge account dinmu .

ABDUSSALAM ABDULLAH

22-1-1448H
7-7-2026.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Address


Kano