Labaran wasanni
domin zafafan labaran wasanni kui mana follow da like
03/06/2026
🚨🔥 SABABBIN DOKOKIN KOFIN DUNIYA NA 2026 DA FIFA TA TABBATAR! 🌍🏆
An tabbatar da wasu manyan sauye-sauye da za su fara aiki a gasar Kofin Duniya ta 2026. Ga dokokin da za su iya sauya yadda ake buga ƙwallo gaba ɗaya! 👇
⏳ JIFAR KWALLO (THROW-IN) – SAKANNI BIYAR 5 KACAL!
Idan ɗan wasa ya yi gangancin ɓata lokaci wajen jefa ƙwallo, alkalin wasa na iya bai wa abokan hamayya ƙwallon.
🥅 BUGUN GOAL-KICK – SAKANNI BIYAR 5 KACAL!
Haka nan idan an yi gangancin ɓata lokaci yayin bugun goal-kick, ana iya hukunta ƙungiyar da ba wa abokan hamayya bugun kusurwa (corner kick).
🔄 CANJIN ƊAN WASA – SAKANNI GOMA 10 KACAL!
Ɗan wasan da ake cirewa yana da daƙiƙa 10 ne kawai ya fita daga filin wasa ta mafi kusa hanya. Idan ya ƙi fita cikin lokaci:
❌ Sabon ɗan wasan ba zai shiga ba na tsawon minti daya 1.
⚠️ Kuma ƙungiyarsa za ta ci gaba da wasa da mutum 10!
🏥 JINYAR ƊAN WASA A WAJE – MINTI 1!
Duk ɗan wasan da likitan ƙungiya ya kula da shi a filin wasa dole ya kasance a waje na tsawon daƙiƙa 60 kafin ya dawo. Sai dai akwai wasu keɓancewa ga masu tsaron gida da wasu yanayi na musamman.
🤐 RUFAR BAKI YAYIN MUHĀWARA? JA KATI NA IYA BIYO!
Idan ɗan wasa ya rufe bakinsa yayin wata takaddama ko muhawara da abokin hamayya, alkalin wasa na iya hukunta shi har da jan kati!
📺 VAR ZAI IYA BINCIKEN CORNER KICK
Na'urar VAR za ta iya tabbatar da ko an bayar da corner daidai ko akasin haka kafin a ci gaba da wasa.
🟨🟥 ZA A IYA SAKE DUBA JA KATIN DA YA FITO DAGA YELLOW BIYU
Idan an kori ɗan wasa saboda yellow cards biyu, za a iya sake duba yellow na biyu domin tabbatar da hukuncin ya dace.
👀🔥 Wadanne daga cikin waɗannan sabbin dokoki ne kuke ganin za su fi kawo cece-kuce a Kofin Duniya na 2026?
Ku bayyana ra'ayinku a comments! ⬇️💬
01/06/2026
🚨🔥 ABIN MAMAKI! Sir Alex Ferguson Ya Aike da Saƙon taya murna Ga me kungiyar PSG Bayan Lashe Champions League! 🏆🇫🇷
Tsohon kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson, ya taya shugaban PSG, Nasser Al-Khelaïfi murnar lashe kofin UEFA Champions League.
A cewar rahoton L'Equipe, Ferguson ya ce:
🗣️ "Nasser, Alex Ferguson ne. Ina Taya murna! Dare ne mai wahala a gare ku, amma kunyi kokari sosai kun buga wasa da ƙungiyar da ba abunda ta iyayi sai zama a baya, wasa mai gajiyar kallo wadda ba ta yi komai ba face kare gida (defending)."
👀 Ferguson ya ƙara da cewa:
🗣️ "Ka ji daɗin hutunka, ka cancanci hakan!"
🏖️ Bayan shekaru da dama na ƙoƙari, PSG ta cimma burinta na ɗaga kofin Champions League, lamarin da ya sa fitattun mutane a duniyar ƙwallon ƙafa ke ci gaba da aika saƙonnin taya murna.
💬 Mene ne ra'ayinku kan kalaman Ferguson? Ku faɗa mana a ƙasan comment! 👇🔥
23/05/2026
Akwai yiwuwar Vini jr yabar Real Madrid, sai dai ko ze bari ba free yakeson ya tafi ba yanaso madrid su amfana da kudin sai da shi, domin tayin albashin da Real madrid ba lale yai masa ba fawn miiyan ashirin £20M yayi kadan, duba da Vini din yaso albashinsa yakai na Mbape koma yafi a wasu majiya yacce s**a ruwaito 🔝
20/05/2026
🇳🇬🔥DAN WASAN NIGERIA MADUKA OKOYE YA GIRGIZA ITALIYA — AN BA SHI KYAUTAR GWARZON ƊAN WASAN UDINESE NA KAKAR WASAN BANA! 🧤⚽️🏆
Mai tsaron ragar Najeriya, Maduka Okoye, ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan ƙungiyar Udinese na kakar wasan bana, bayan nuna bajinta mai ban mamaki a gasar Serie A ta ƙasar Italiya. 🎊🥳🇳🇬
Okoye ya kasance tamkar bango a ragar Udinese tsawon kakar wasan, inda ya yi “clean sheet” sau 10 cikin wasanni 29 da ya buga a ɗaya daga cikin mafi tsauraran gasar League na ƙwallon ƙafa na duniya. 💪🏾🧤
Daga cikin manyan wasannin da ya haskaka akwai fafatawar da s**a yi da manyan ƙungiyoyi kamar Juventus da AC Milan, inda ya nuna ƙwarewa da jajircewa da s**a burge magoya baya da masana ƙwallo. ⚡🔥
Ba nan kawai ya tsaya ba — an kuma saka sunansa cikin jerin ‘yan wasan da aka zaɓa domin kyautar gwarzon ɗan wasan watan Mayu na Serie A. 👏🏾✨
Lallai wannan kaka ta zama ta tarihi ga Maduka Okoye da kuma ƙwallon ƙafar Najeriya baki ɗaya. ❤️🇳🇬
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Telephone
Website
Address
Kano
Kaduna