YOLA TIMES

YOLA TIMES

Share

Media/news

16/09/2023

Memene amfanin group dinnan a matsayinmu na en yola bamu San sunan juna ba drop your name for comments section👇👇👇?

04/06/2023

WALITAKAR ALBANIY DA JA'AFAR TA BAYYANA

Zan fara da Baffa Hotoro wanda yake jingina kansa da da'awar Sunnah Salafiyyah

Lokacin da Baffa Hotoro ya bayyana, yana son a sanshi yayi suna, sai ya dauki hanyar zakulo maganganun Marigayi Sheikh Ja'afar da Sheikh Albaniy Zaria yana datsewa yana musu sharri da kage yana ciresu daga da'irar Sunnah yana alakanta musu ta'addanci da kungiyar Boko Haram

Ina tuna lokacin da Sheikh Dahiru Usman Bauchi yake kafa hujja da maganar Baffa Hotoro akan batanci da sharrin da yayi wa Shahidanmu Malam Ja'afar da Albaniy, to wannan yana daga cikin munin barnan da Baffa Hotoro yayi wa da'awar Malam Ja'afar da Albaniy don neman a sanshi, saboda 'yan bidi'ah kan kafa hujja da maganganun batancin da ya yiwa su Malam Ja'afar

Da Allah Ya tashi k**a Baffa Hotoro, sai ya k**ashi ta hannun makiyan su Malam Ja'afar inda shi Baffa Hotoron ya tsallaka kan Sheikh Dahiru Bauchi yaci mutuncinsa, su kuma iyalan Sheikh Dahiru s**ayi karansa, DSS s**a masa damka mai karfi har da leg-chain a kafarsa, ya fito a bidiyo yana basu hakuri, to ba komai bane alhakkin su Malam Ja'afar ne da Albaniy ya k**ashi, watakila hakan ya zama sanadin shiriyarsa

Sai ga wani yaro a Bauchi daga bangaren sufaye Abulfathi Attijjaniy ya bayyana, yana ta zagi da cin mutuncin Malaman Sunnah, kai tsaye ya fito yace su Albaniy da Ja'afar 'yan ta'adda ne sun karantar da ta'addanci bayan ya kudunduma musu buhunan ashariya ana ta buga masa kabbara yana kwaba

Daliban Malam Albaniy s**a yi karansa gurin shugaban 'yan sandan Nigeria IGP, 'yan sanda sun k**ashi don gudanar da bincike kafin a tafi Kotu, shine yayi bidiyo babu riga dagashi sai singilet yana bada hakuri don ya san zai dauru igiya sai ya saura, to wannan bidiyon yayi a kansa ne, amma Kotu kam sai ya je, don ba'a hakura ba

Wannan duka alamace da take tabbatar mana da cewa su Malam Albaniy Zaria da Malam Ja'afar Waliyyai ne, Malaman Allah ne, basu karantar da ta'addanci ba, sun yaki ta'addanci ne, akan fada da ta'addanci da su

19/05/2023

Gwamna Matawalle ba zai ce komai ba a yanzu kan zargin wawure kuÉ—in talakawa biliyan N70bn.

Kakakin gwamnan, Zailani Bappa, ya ce a halin yanzu mai gidansa da shirin barin gadon mulki.

Nan da kwana 10 wa'adin Matawalle zai kare bayan faÉ—uwa a babban zaben 2023.

Want your business to be the top-listed Media Company in Yola?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address


Sokoto Street Yola Town
Yola
640102