Sadiq Ango Abdullahi
Member House of Representatives Sabon Gari Federal Constituency
Deputy Chair House Committee on FERMA
27/05/2026
Alhamdulillah!
A yau na samu damar gudanar da Sallah Eidi a mazabata , Hanwa Makera gundumar Hanwa tare da al'umma ta na wannan yanki namu mai albarka.
Na gabatar da wannan sallah ne tare da mai girma Madakin Zazzau, Alh. Munir Jafaru tare da Sarkin Hanwa da babban limamin garin hanwa da sauran manyan mutane da sarakuna hadi da malamai da sauran al'umma baki daya.
Hakika anyi zumunci an yi gaishe -gaishe hadi da addu'o'in fatan alkhairi ga juna da jihar mu da Kasar mu Nigeria baki daya.
Allah Ya amsa mana dukkanin ibadun mu ya maimaita mana cikin koshin lafiya da yalwan arziki. Ameen.
Barka da Sallah.
Hon. Sadiq Ango Abdullahi
Member, Representing Sabon Gari Federal Constituency
Deputy Chairman, House Committee on FERMA
27th May, 2026
27/05/2026
EID EL-ADHA
I join the entire Muslim Ummah in wishing all Muslims and the good people of Sabon Gari Federal Constituency a blessed and joyful Eid Mubarak.
As we celebrate this sacred Eid, May the spirit of Eid bring unity, compassion, and happiness to our lives. May Allah grant us all goodness in dunya and akhirah. Ameen.
To the good people of Sabon Gari Federal Constituency, I sincerely appreciate the trust, prayers, support, and goodwill you have continued to show me. I have never taken it for granted, and I remain committed to doing my very best in delivering the dividends of democracy and quality representation to our constituency.
Eid Mubarak once again.
HAUSA
SAKON BARKA DA EID EL-ADHA (BABBAN SALLAH)
Ina taya daukacin al’ummar Musulmi musamman al’ummar Mazabar Tarayya ta Sabon Gari murnar babbar Sallah cikin farin ciki da albarka. Allah Ya maimaita mana ita cikin zaman lafiya da wadata.
Yayin da muke gudanar da wannan ibada mai albarka, ina addu’ar Allah Ya sanya ruhin wannan Sallah ya kawo hadin kai, tausayi da farin ciki a rayuwarmu. Allah Ya ba mu alherin duniya da lahira baki daya. Ameen.
Ga al’ummar mu masu albarka na Mazabar Tarayya ta Sabon Gari, ina matukar godiya da irin amincewa, addu’o’i, goyon baya da kyakkyawar niyya da kuke ci gaba da nuna mini. Ban taba daukar hakan da wasa ba, kuma zan ci gaba da yin iyakar kokarina wajen samar da ribar dimokuradiyya da ingantacciyar wakilci ga mazabarmu.
Ina sake taya kawunan mu murnar Babbar Sallah.
Hon. Sadiq Ango Abdullahi
Member, House of Representatives
Sabon Gari Federal Constituency
Deputy Chairman, House Committee on FERMA
27th May 2026
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Telephone
Website
Address
Zaria